Dogo Gide Na Neman N100m Kan Daliban FGC Birnin Yauri
Iyayen daliban da aka sace a Sakandaren Gwamnatin Tarayya (FGC) ta Birnin Yauri a Jihar Kebbi na neman agaji, bayan dan ta’addan da ya sace su, Dogo Gide, ya sa musu kudin fansa Naira miliyan 100.
Dogo Gide ya sanya sharadin biyan Naira miliyan 100 ne duk da iyayen yaran sun bi ta hannun mahaifiyarsa ta matsa masa lamba ya sako ragowar ’yan mata 11 da ke hannusa kusan tsawon shekara biyu.
Maharan jirgin Edo na neman fansar N520m
NAJERIYA A YAU: Ma’aikatar Shari’a ta fadi gwajin tsare gaskiya —ICPC
“Mun yi magana da Dogon Gide ranar 15 ga wagan Disamba, 2022, da farko ya ki magana, amma bayan mahaifiyarsa ta sa baki, ya amince zai sako yaranmu idan mun biya Naira miliyan 1oo, ko kuma mu hakura da su.
“Ya fada karara cewa idan ba mu yi abin da ya ce ba, har abada ba za mu sake jin duriyar ’ya’yanmu ba,” in ji Shugaban kungiyar iyayen daliban, Salim Kaoje.
Ya bayyana haka ne a wani taro da suka yi a makarantar a ranar Lahadi, inda suka ce sun riga sun ga gazawar gwamnati wajen ceto musu ’ya’ya, don haka ba su da zabi face yin abin da suke ganin za su iya.
Kusan shekara biyu ke nan, a watan Yunin 21, ’yan bindiga suka kai hari Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya ta Birnin Yauri suka yi awon gaba da dalibai 80, kuma har yanzu suna tsare da 11 daga cikin yaran.
Kaoje ya ce hakan ne ya susuke karo-karo daga hannun jama’a don tara kudaden da dan ta’addan ya shardanta, “shi ya sa muka zo domin yin wannan roko.”
Kaoje ya ce kowanne daga cikin iyayen daliban ya amince ya sayar da duk kadarorinsa domin su hada kudaden.