Labari Da Dumiduminsa: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kamfanonin Jiragen Da Zasu Yi Jigilar Maniyyata Hajin 2024
Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da wasu manyan kamfanonin jiragen sama guda uku da za su yi jigilar maniyyata aikin hajjin 2024, wadanda suka hada da Air Peace., FlyNas da Max Air. Har ila yau, an amince da wasu kamfanoni uku na jigilar kayayyaki da za su yi jigilar kayan alhazai Waɗannan su ne Cargo Zeal Technologies Ltd, Nahco Aviance da Qualla Investment Limited. A sanarwar da mataimakiyar daraktar harkokin hulda da jama'a da dab'i ta hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace Yarjejeniyar ta karfafa yunƙurin gwamnati na tabbatar da ingantaccen aikin hajji ga maniyyatan Najeriya. Don haka, a lokaci guda gwamnatin tarayya ta amince da rabon maniyyata daga jahohi daban-daban ga kowane kamfanonin jiragen sama da aka amince da su kamar haka: i.Air Peace zai yi jigilar maniyyata daga: Abia, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, FCT, Imo, Kwara, Ondo da R...