Posts

Showing posts with the label Kiwon Lafiya

Tsananin Zafi: An Buƙaci Mutane su Ɗauki Matakan Kariya na Kiwon Lafiya

Image
Yayin da ake yanzu haka ake fama da tsananin zafin, an yi kira ga al’umma da su ɗauki matakan kariya na kiwon lafiya domin kare lafiyarsu daga faɗa wa haɗari. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar, Ibrahim Abdullahi ya sanyawa hannu, yace Kwamishinan Lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi kiran a cikin wata sanarwar manema labarai da ta fito a yau Alhamis daga sashin yaɗa labarai na ma’aikatar, aka raba wa kafafen sadarwa. Dakta Labaran ya ce yanayin zafin da ake ciki ya fara ne tun daga watan Maris na wannan shekara, wanda ya sanya ƙaruwar zazzaɓi da mace-mace, ya ƙara da cewa tun daga lokacin ma’aikatar lafiya ta shiga binciken gano haƙiƙanin abin da ke faruwa.  Kwamishinan ya yi nuni da cewa al’ummar Kano sun san waɗannan watanni guda uku – Maris, Afrilu da Mayu, har ma da farkon watan Yuni – watanni ne na ta’azzarar zafin rana, da hakan ke janyo abubuwa masu yawa da suka haɗa da ƙaruwar zazzaɓin cizon sauro da cutar sanƙara...