Posts

Showing posts with the label 1993

Kamawa zasu maimaita abun da ya faru a zaben 1993 - Ganduje

Image
Abdullahi Umar Ganduje, ya ce Kanawa za su sake maimaita abin da ya faru a zaben Shugaban Kasa na 1993, inda suka goyi bayan dan takarar da ya fito daga yankin Kudu – suka yi watsi da nasu na Arewa kuma dan asalin jihar. Ganduje ya yi wannan furuci ne a yayin wani rangadin yakin neman zabe da ya fita tare da ’yan takarar jam’iyyar APC masu neman mukamai daban-daban a zabe mai zuwa. Aminiya ta ruwaito cewa gwamnan ya yi furucin ne yayin da ya ziyarci Hakimin Kibiya, Sunusi Abubakar Ila, bayan gudanar da taron yakin neman zabe da tuntubar juna a kananan hukumomin Rano da Bunkure na jihar. A zahiri dai Ganduje ya tabbatar da goyon bayansa ga dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, inda ya yi hannun riga da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ke takarar kujerar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP. A jawabinsa yayin hikaito tarihi, Ganduje ya ce, “Mun zabi Cif MKO Abiola na jam’iyyar SDP kuma muka ki amincewa da Bashir Othman Tofa na jam’...