Posts

Showing posts with the label Hisbah

Hisbah Ta Haramta Wa Maza Yin DJ A Tarukan Mata A Kano

Image
Sheikh Daurawa ya ce yin hakan ya zama dole don rage cakuɗuwar maza da mata a wuraren bukukuwa Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta sanar cewa daga yanzu an haramta wa maza yin aikin DJ a tarukan mata a jihar. Shugaban Hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya sanar da hakan ne a lokacin ganawarsa da ƙungiyoyin masu sana'ar kida na DJ. Malamin ya bayyana cewa yin hakan ya zama dole ne rage cakuɗuwar maza da mata a wurin bukukuwa a Jihar Kano. (AMINIYA)

Hisbah Ta Wanke Matar Da Ta Auri Saurayin ’Yarta A Kano Daga Zargi

Image
  Kwamitin da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kafa kan binciken auren matar da ta auri saurayin ’yarta, ya wanke ta daga zarge-zargen da ake mata. Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Alhaji Lawan Ibrahim ya fitar a Kano a ranar Talata. Sanarwar ta ce “Gabatar da rahoton binciken da kwamiti ya ya yi karkashin jagorancin Kwamanda Malam Hussain Ahmed, an gano auren halal ta yi kuma ta cika duk wasu sharuda da addini ya tanadar.” Sanarwar ta kuma ce bincikensu ya nuna cewar matar mijinta ya sake ta tun da fari kuma ta yi iddar wata uku kamar yadda addinin Musulunci ya tsara, kafin daga bisani ta auri saurayin ’yarta da ta daina so. Mataimakin Kwamandan ya yi watsi da zargin da ake wa matar na cewar ita ta kashe aurenta don ta auri saurayin ’yarta. “Auren halal suka yi kamar yadda Musulunci ya tsara, shi ya sa Kwamandan Hisbah a Karamar Hukumar Rano ya jagoranci daurin auren.” Babban Kwamandan Hukumar Hisbah na Jihar, Harun Ibn-Sina, ya jinjina wa kwamitin kan yadda suka gu...

Hisbah Ta Rufe Wuraren Shan Giya Sama Da 100 A Zariya

Image
Wata kungiyar addinin Musulunci mai zaman kanta mai suna Hisbah, ta jagorance garkame wuraren shan giya sama da 100 a Karamar Hukumar Sabon Gari da ke Jihar Kaduna. Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Sabon Gari, Garba Datti Babawo ne ya tabbatar da hakan, yayin gabatar da hsaidar kammala karbar horo ga ’yan kungiyar su 750 da ya gudana a hedkwatar Karamar Hukumar ta Sabon Gari. Dan majalisar ya ce tun da Karamar Hukumar take ba ta taba samun sa’ida daga ayyukan badala ba sama da lokacin da aka kafa rundunar ta Hisbah. Daga nan sai Babawo ya ja kunnen dakarun da su tabbatar suna bin dokokin dokoki yayin gudanar da ayyukansu. Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar ta Sabon Gari, Injiniya Mohammed Usman, ya jaddada kudurin gwamnatinsa na kakkabe yankin daga ayyukan masha’a, ta yadda za a sami yanayin kasuwanci mai kyau tare da bunkasa zaman lafiya a tsakanin al’umma. Tun da farko sai da Kwamandan rundunar a yankin, Abubakar Auwal ya ce dakarun su 750 su...