Search This Blog

Tuesday, 26 December 2023

Hajj 2024 : Hukumar Alhazai Ta Bauchi Ta Siyar Da Kujerun Haji Guda 1700- Imam Abdurrahman

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Bauchi ta sayar da kimanin guraban kujerun aikin hajji akalla *1700* daga cikin guda *3364* da Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ware wa Jihar Bauchi.

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Muhammad Sani Yunusa ya sanyawa hannu, yace Sakataren zartarwa na hukumar jindadin alhazan ta jihar Bauchi Imam Abdurrahman Ibrahim Idris,shi ne bayyana hakan yayin  zantawarsa da manema labarai kan shirye shiryen aikin hajji daga Bauchi, inda yace wayarda alumma kan sabbin tsare tsaren aikin hajjin na shekarar 2024 daya gudana a jihar Bauchi yayi tasiri kwarai da gaske.

Imam Abdurrahman ya alakanta nasarar gudanar da atisayen wayarda kan alummar ne da irin gudumawa da goyon bayan da tsarin ya samu daga sarakunan mu na jihar Bauchi da shugabannin kananan hukumomi da limamai da sauran masu ruwa da tsaki a aikin Hajji.

Ya kara da cewa sabbin tsare-tsare na Saudiyya kan ayyukan Hajji na shekarar 2024 ne suka tilastawa kasashe fara  shirye-shiryen ayyukan Hajjinsu da wuri.

 Imam Abdurrahman ya ci gaba da tunatar da cewa NAHCON ta sanya *N4.5M* a matsayin kudin ajiya na bana tare da bayar da wa'adin watan Disamba na tura kaso na farko daga dukkan Jihohin a kasa domin su kare  gurbin kujerun  aikin Hajji da aka ware musu.

A cewar sa "a baya dai mun aiyana karshen watan Disamba na 2023 a matsayin wa'adin karban kudin ajiyar aikin hajjin 2024, zamu saurari hukumar alhazai ta kasa don jin umurni na gaba"

Imam Abdurrahman ya shawarci maniyyata dasu yi anfani da wannan lokaci na musamman wajen cikita kudin ajiyarsu na N4.5M, harilayau sabbin masu biya, suma dama ce garesu dasu biya kudin ajiyar tasu.

 

Wednesday, 20 December 2023

Shugaban Majalisar Dokoki Ta Katsina Ya Raba Tallafin Naira Miliyan 35

Kakakin Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina, Nasir Yahaya, ya bayar da tallafin Naira Million Talatin da Huɗu da Dubu Ɗari Tara da Hamsin. (34,950,000) ga Mutum Dubu Ukku (3000) a filin wasan Ƙwallon Kafa dake Daura

Hadimin tsohon Shugaban Najeriya, Buhari Sallau, ya rawaito a shafinsa na Facebook cewa, an bayar da Tallafin ga Marayu, Limamai, Zawarawa, Masu Ƙananan Sana'oi, Exco, Mata, Matasa, Students, yan Media, Dagattai, Mabuƙata, yan siyasa, Ƙungiyar Teloli, Ƙungiyar Masu Shayi da Masu chajin waya, da sauran su. Inda ko wanne daga cikinsu zai amfana da Tallafin, Naira Dubu Goma (10,000)

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda PhD, yayi Jin-Jina gami da fatan Alkhairi ga Kakakin Majalissar akan wannan abin Alkhairi da yayi, sannan yayi roƙo gami da Jan hankali ga wanda suka amfana da wannan Tallafin da suyi amfani dashi ta hanyar daya dace, domin su bunƙasa Kasuwar su. 

Haka kuma Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC na Jihar, Alh. Bala Abu Musawa, ya taya mutanen Daura murna, bisa ga Jajirtaccen Shugaba da suka samu.

Taron ya samu Halartar Tsohon Shugaban Ƙasar Nigeria, Gen. Muhammadu Buhari, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa PhD, Shugaban Jam'iyyar APC na Jiha da Mataimakinsa, Yan Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina, kwamishinoni da masu bada shawara, Wakilin Mai Martaba Sarkin Daura, Hajia Ambarud Sani Wali, Shugaban karamar hukuma, Tsofaffin yan Majalissar Jiha, Barr. Ahmad Usman El-Marzuq, da sauran manyan baƙi

Kakakin Majalissa ya bayar da kyautar Sa (Bijimi) ga Muhammadu Buhari, da kyautar Doki ga Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa. 
 
Sannan Ƙungiyoyin Daura Forum, DECA, DEDA, Health and Education Department, Ƙungiyoyin Addini, da Babbar Ƙungiyar, Daura Consortium sun bayar da Lambobin Yabo da Girmamawa (Award) ga Mai Girma Kakakin Majalissar Dokoki a bisa ayyukan Alkhairin da yake aikatawa ba dare ba rana a Daura

Haka zalika Ƙungiyar Daura Forum ta bada lambar yabon ga  Muhammadu Buhari, da Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa  

Daga karshe Kakakin Majalissa yayi Godiya ga manyan baƙi da suka halarci wannan Babban taron, sannan yayi Addu'a da fatan Allah ya maida kowa gidanshi lafiya, l

Shugaban NAHCON Ya Ziyarci Ofishin Jakadancin Saudiyya na Abuja.

Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya wato NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya kai ziyarar ban-girma zuwa ofishin Huldar Jakadanci na Saudiyya inda ya gana da Jakadan Saudiyya dake Abuja, Ambasada Faisal Ibrahim Al-Ghamidy, a ranar Laraba  

A sanarwar da Hukumar ta fitar ta ce, Shugaban ya kai ziyarar ce da nufin bunkasa dangantaka da habakar da hadin-gwiwa tsakanin bangarorin biyu.
 
Malam Arabi ya jaddada jin dadinsa ganin yadda Jakadan Kasar Saudiyya Ambassada Faisal ke bada cikakken goyon-baya ga Hukumar da tareraya irinta Huldar Jakadanci karkashin  Ofishin Jakadancin Saudiyyar.

Sanarwar tace ziyarar, ta bayyana karara yadda dadaddiyar alaqa ta jituwa ke tsakanin NAHCON da Ofishin Jakadancin Saudiyyar, abinda ke nuni da fahimtar-juna da hadin kai dake wanzuwa a tsakanin Kasashen biyu.

A Yayin ganawar, bangarorin biyu
 sun zanta batutuwa masu ma’anar gaske, abunda ke tabbatar da muhimmancin tarayyarsu wajen kara inganta gudanar da Al-amurran Aikin Hajji A Najeriya

Shugaban NAHCON ya bayyana jinjinarsa ga cigaba da habakar da temakekeniyar da Ofishin Jakadancin Saudiyya ke baiwa Hukumar Hajjin, abunda ke haifar da samun nasarar gudanar da Aikin Hajji cikin walwala da dadin-rai ga Alhazan Najeriya. 

Bisa wannan ci gaba, bangarorin guda biyu sun sha  alwashin kara jajircewa da yin tsayin-daka wajen ganin sun kara zama tsintsiya madaurinki daya wajen aiwatar da hadahadar Aikin Hajjin tare da cikakken hadin-gwiwa da zai cigaba da samar da sakamako melai dorewa da wanzar da ingantaccen Hajji ga Alhazai da sauran masu ruwa da tsaki a Harkar Gudanar da Hajji.

Wannan hadin gwiwa dake tsakanin NAHCON da Ofishin Huldar Jakadancin Saudi Arabiya, zai ci gaba da share fagen ingantuwar kai kawo da musayar bayanai da samar da walwala ga dubban Alhazai Maniyyata zuwa Ibadar Hajji. 

Hakazalika, Sun daura azama da aniyar gaggauta hanyoyin samarwa Maniyyata jin dadi yadda ya kamata.

A wani ci gaba kuma, nan ba da jimawa ba ne, Hukumar NAHCON  zata kammala bincike-binciken korafe-korafen da kamfanonin jirgin yawo suka gabatar a gabanta don tabbatar da ganin wadanda aka tantance ba suda wata matsala domin su gudanar da kai Alhazan shekarar bana ta hanyar jiragen-yawo lami lafiya. 
 
Za a iya tunawa ranar sha uku ga watan nan na Disamba, NAHCON ta sanar da dakatarwa ta wani dan-lokaci don tsagaita raba kujerun tafiya Hajjin bana ga kampanonin-jigilar Maniyyata. Anyi hakan don kwatanta rabo na Allah da Annabi, biyo bayan korafe-korafe da suka bijiro daga wasu bangarori. 

Sanarwar tace NAHCON na nan kan wannan tsaikon har sai ta tabbatar da gaskiyar lamari don samun Rabo na gaskiya ga dukkan kamfanonin na jigilar Alhazan.


Monday, 18 December 2023

Kotun Koli Ta Tsayar Da Ranar Da Za Ta Saurari Karar Zaben Gwamnan Kano

Kotun koli ta sanya ranar Alhamis 21 ga watan Disamba domin cigaba da sauraron karar zaben gwamnan Kano tsakanin gwamna Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC. 

KANO FOCUS ta rawaito cewa a cikin sanarwar da magatakardar kotun daukaka kara ta aikewa lauyoyin bangarorin biyu, kotun za ta saurari karar da NNPP ta shigar da kararrakin wasu jam’iyyu. 

Gwamna Yusuf na kalubalantar hukuncin da wasu bangarori uku na kotun daukaka kara suka yanke wanda ya soke nasarar da ya samu tare da tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke. Kotun sauraron kararrakin zabe karkashin jagorancin mai shari’a Osedebay ta bayyana dan takarar jam’iyyar APC, Nasiru Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano a watan Maris. 

Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar da Gwamna Yusuf ya shigar bisa matsayinsa na zama mamba a jam’iyyarsa sannan ta zargi kotun da yin watsi da hujjar da ta yanke. Kotun ta kori Gwamna Yusuf ne saboda amfani da takardun zabe da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ba ta sa hannu, ko kwanan wata ko tambari ba. 

An dai samu rudani a dukkan shari'ar yayin da NNPP ta gano hujjojin da CTC na kotun daukaka kara da ta tabbatar da Gwamna Yusuf a matsayin wanda ya lashe zaben, wanda ya sabawa abin da alkalan kotun suka karanta. Raba wannan: 
 

Sunday, 17 December 2023

Kofa Ya Raba Tallafin Kudi Ga Mata Guda Dari Biyar A Mazabarsa

A ci gaba da tagomashin arzikin da yake yi wa mutanen mazaɓarsa, Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan Majalisar Wakilai na Kiru da Bebeji daga jihar Kano, a ranar Lahadi ya sake gwangwaje mata 500 da tallafin kuɗi.

A sanarwar da hadimin ɗan majalisar kan yaɗa labarai, Sani Ibrahim Paki ya fitar, yace an  yi taron rabon tallafin ne a mahaifar ɗan majalisar da ke Kofa a Ƙaramar Hukumar Bebeji, Kano, kuma wannan shi ne karo na bakwai da yake raba irin wannan tallafin a ’yan makonnin nan. 
Idan za a iya tunawa, a baya ɗan majalisar ya raba tallafin ga shugabannin al’umma, mata da matasa, ɗalibai, ’yan social media, malamai da masu rike da sarautun gargajiya. 

Wannan ne dai rabon tallafi karo na bakwai tun bayan farawa, kuma karo na biyu ga mata.
Bugu da ƙari, ɗan majalisar ya karɓi baƙuncin fitacciyar ’yar asalin Bebejin nan, kuma jigo a jam’iyyar NNPP, Hajiya Azumi Babeji, wacce ita ma ta halarci bikin sannan ta gabatar masa da takardar nadin da Gwamnatin Jihar Kano ta yi mata. 
Dan majalisar ya mika godiya ga gwamnatin saboda ganin cancantarta har ta ba ta wannan muƙamin.


Friday, 15 December 2023

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Yi Ga NAHCON Da Ta Samar Canjin Dala Kan Farashin Gwamnati Ga Maniyyata

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, ya bukaci Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta kara zage damtse wajen ganin an samu dala a farashin gwamnati  ga wadanda zasu halarci aikin hajjin bana.

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bayyana hakan ne a wata ganawa da kungiyar Arewa New Agenda a wata ziyarar wayar da kai da hukumar alhazai ta kasa suka kai Kano, wanda aka gudanar  a ofishinsa.

Ya kara da cewa karin kudin aikin Hajjin bana da kuma karancin lokacin biyan kudi na daga cikin matsalolin dake kawo tsaiko wajen biyan kudaden ajiya.

Da yake mayar da jawabi kan wadannan matsalolin, shugaban tawagar kungiyar Arewa New Agenda daga Hukumar Alhazai ta kasa, Dakta Muhd Lawan Salisu, ya tabbatar wa darakta Janar din cewa, sun dukufa wajen hada kai da hukumomin da abin ya shafa, ciki har da Sarkin Musulmi, domin mika kokon bara ga shugaban kasa kan wannan bukata. na tallafin aikin Hajji.

Dokta Muhd Lawan Salisu ya yi alkawarin binciko duk hanyoyin da za a bi domin saukaka samun sauki da samun saukin kwarewar aikin hajji.

A nasa jawabin shugaban hukumar, Yusif Lawan ya ce hukumar ta ci gaba da dukufa wajen tabbatar da jin dadi da walwala ga dukkan mahalarta aikin Hajji, tare da yin aiki kafada da kafada da hukumar alhazai ta kasa domin magance kalubale da habaka aikin hajjin baki daya.

Taron ya samu halartar dukkan ma’aikatan hukumar, da jami’an Hukumar na kananan hukumomi da wasu daga cikin malaman bita 


                  

Thursday, 14 December 2023

Gwamnatin Kano Ta Tabbatar da Gano Illar Bata Tarbiyya Yara Mata A Shirin Tallafawa Ilimi Na AGILE

Biyo bayan zarge-zargen bata tarbiyya da ake yiwa shirin tallafawa ilimin yaya mata na AGILE, ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta gudanar da taron karawa juna sani na yini biyu kan shirin.

Premier Radio ta rawaito a shafinta na Facebook cewa, Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, wanda ya yi magana a yayin taron na masu ruwa da tsakin da ke nazarin horar da dabarun rayuwa a karkashin shirin, ya ce ma’aikatar ta fitar da wani sabon salo na abubuwan da shirin ya kunsa.


Ya ce malamai sun yi korafin cewa a cikin shirin akwai wasu abubuwa da basu amince da su ba inda suka duba korafin nasu kuma suka gano matsalar dake cikin sa yayin da aka cire duk wani da ya saba da al’ada da koyarwar addnini muslunci.

A nashi bangaren, co’odinetan shirin na AGILE a nan Kano, Alhaji Nasiru Abdullahi-Kwalli, ya ce ma

NAHCON Ta Dakatar Da Rabon Kujeru Ga Kanfanonin Jirgin Yawo

Hukumar Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) a dakatar da rabon kujeru aikin Hajjin 2024 ga kamfanonin jirgin yawo 40 da suka yi nasarar samun aikin jigilar maniyyata.

NAHCON ta dakatar da rabon kujerun ne saboda korafe-korafen da zargin rashin adalci da wasu kamfanonin da ba su yi nasara ba ke yi.


Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce hukumar na sane da irin wadanna zarge-zarge daga wasu kamfanonin da ba su yi nasara a tantancewar da aka yi ba.

Don haka aka dakatar da akai na tsawon awa 48 masu zuwa, domin daukar matakin da ya dace, tabbatar da tsafta a aikin da kuma kare martabar kukumar.
(AMINIYA)


Wednesday, 13 December 2023

Na shiga matsananciyar damuwa da hare-haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan - Gwamnan Zamfara

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook

Inda yace "A madadin gwamnatin Jihar Zamfara, ina miƙa saƙon ta'aziyya da jaje ga al'ummar ƙaramar hukumar Zurmi, musamman iyalai da ‘yan uwan waɗanda suka rasa rayukansu a harin ta'addanci da 'yan bindiga suka kai garin" 

Ina son tabbatarwa da al'umma cewa gwamnatina za ta bayar da tallafi da agajin gaggawa ga mutanen da abin ya shafa. Sannan ina mai tabbatar da cewa muna nan jajirce akan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar Zamfara baki ɗaya.

Ina sane da sadaukarwar da jami’an tsaro suke yi a ƙoƙarin da suke na kare rayukan al’umma, gwamnatina za ta ba su duk wasu kayan aiki da kuma tallafin da suka dace domin yaƙar ‘yan bindiga, ba za mu huta ba har sai Zamfara ta samu cikakken tsaro insha Allahu.
 
Waɗannan sabbin hare hare sun biyo bayan nasarar da jami'an tsaro suka samu ne, na kashe shugabannin 'yan ta'addan. Ciki har da nasarar kashe Kachalla Ali Kawaje, Shugaban ‘yan bindiga da ya jagoranci sace ɗaliban jami’ar tarayya dake Gusau.
 
An samu nasarar kawar da shugabannin ɓarayin da dama a wurare daban-daban da suka haɗa da Danjibga, dajin ‘Yar tsakuwa, dajin Munhaye, dajin Kauran Zomo, dajin Dansadau, da kauyen Akuzo.
 
Ina sake jaddada wa al'ummar Jihar Zamfara cewa, da yardan Allah zan ci gaba da bin dukkan matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya a faɗin jiharmu mai albarka.

Shugaban Hukumar NAHCON Ya Karbi Rahoto Kan Masaukin Alhazai Tare Da Alkawarin Sake Inganta Ayyuka

Mai rikon mukamin Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Malam
Jalal Ahmed Arabi, OON, fwc, ya ce ba da fifiko tare da inganta jin dadin mahajjata da ayyukansu shi ne babban aikin da Hukumar za ta gudanar a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024.

A sanarwar da Mataimakin daraktan yada yada labarai da dab'i na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar rahoton kwamitin duba sharuɗɗan masauki da ciyarwa yau a dakin taro na hukumar

Ya ce samar da ingantacciyar hidima aiki ne mai matukar muhimmanci da hukumar za ta bi domin cika aikinta tare da dorewar amana da amincewar jama’a da kuma alhazai.
A cewarsa, gabatar da rahoton da shawarwari a cikinsa “zai taimaka matuka wajen farfado da kwarin gwiwa da amincewar mutane da alhazai musamman a gare mu.

“Ina so in gode muku bisa sadaukarwar da kuka yi. Wannan rahoto da shawarwarin ba shakka za su ba da gudummawa don haɓaka hanyoyin ci gaba da aiwatar da abubuwa. Na san cewa babu wani abu mai dorewa a rayuwa kamar canji don haka muna bukatar mu zama masu kirkira ta yadda muke yin abubuwa. Ina mai tabbatar muku da cewa za mu duba tashar jirgin, tare kafin aiwatar da shi domin samun damar samun sauye-sauye masu kyau a yadda muke gudanar da ayyukan alhazai.”

Malam Arabi ya kuma bukaci Hukumar Jin Dadin Alhazai na Jiha da su baiwa hukumar hadin kai tare da marawa hukumar baya a aikinta inda ya ce, “ba wani riba ba ne a ce akwai bukatar karin hadin kai tsakanin Hukumar da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jiha. Ina mai farin cikin ganin cewa wasu daga cikin shuwagabannin hukumar jin dadin Alhazai ta Jiha suna cikin kwamitin, ina fatan za ku mika sakon ga abokan aikin ku cewa suna bukatar yin layi a cikin wasu shawarwarin da kuke bayarwa, kuma ku gamsar da su. shawarwarin da kuka bayar a cikin rahoton shi ne mu sanya yadda muke gudanar da ayyuka cikin sauki da kuma ci gaban kowa."

Tun da farko, Dr Aliyu Tanko wanda shi ne Shugaban Kwamitin ya nuna jin dadinsa da amincewa da aka yi masu. 
Ya bayyana cewa Kwamitin ya ba da shawarwari masu nisa don kawar da shirye-shiryen ciyar da abinci da masauki daga wasu matsalolin.

Za a iya tunawa tuna cewa an kafa kwamitin mai wakilai 16 kuma an kaddamar da shi ne a ranar 5 ga watan Disamba tare da ayyuka kamar haka:
I. Don kimanta jagororin masauki da abinci na yanzu.

II. Don tantance ma'auni na yanzu na mahajjata masauki da ayyuka na ciyar da abinci.

III. Gano wuraren ingantasu

IV. Ba da shawarar sake duba jagororin da za su tabbatar da jin daɗi da ƙwarewa ga mahajjatanmu.


Monday, 11 December 2023

Labari Da Dumiduminsa: 'Yan Majlisar Jahar Rivers 27 Masu Biyayya Ga Wike Sun Bar PDP Zuwa Jam'iyyar APC

Akalla ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas 27 cikin 32 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ministan babban birnin tarayya (FCT). Nyesom Wike ya zurfafa.


Wani dan majalisar, Enemi George, ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan majalisar 27 na karkashin jagorancin Martin Amaewhule ne.

'Yan majalisar sun yanke Wannan hukuncin ne a yayin zamansu na safiyar ranar Litinin

(DailyNews24)

Sunday, 10 December 2023

Gwamnan Katsina Ya Ceto Wanda Yan Ta'adda Suka Sace

Gwamnan Katsina, Dikko Raddah, ya jagoranci fatattar ’yan bidiga a kauyen Zakka a Karamar Hukumar Safana ta jihar.

Gwamnan ya jagornaci jami’an tsaro hadin gwiwa wajen ceto wani matashi da ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi.


Dikko Radda ya jagoranci kai daukin ne a lokacin da ya je karamar hukumar kaddamar da shirin tallafi na mataimakin shugaban majalisar jihar, Abduljalal Runka.

Sakataren yada labaran gwamna, Kaula Mohammed, ya ce kafin kaddamar da tallafin ne jami’an tsaro suka samu kiran gagawa cewa ’yan ta’adda sun kai hari kauyen Zakka.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Kaula na cewa, nan take gwamnan ya dakatar da shirin, shige gaba aka fattaki ’yan bindigar, aka ceto matashin.

Daga nan gwamnan ya ba da umarnin kai mutumin asibiti domin kula da shi, saboda harbin sa da aka yi a kafa.

Sanatoci Sun Sallama Albashinsu Na Disamba Ga Mutanen Tudun Biri

Sanatocin Najeriya gaba dayansu sun sadaukar da albashinsu na watan Disamba ga mutanen da harin bom da jirgin soji ya samu a wurin taron Mauludi a Jihar Kaduna.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya sanar cewa sanatocin su 109 sun amince a ba da albashin nasu a matsayin gudunmuwar ga mutanen Tudun Biri.


Sanata Barau wanda ya yi bayani a yayin ziyararsu fadar gwamnatin Kaduna domin jajanta wa Gwamna Uba Sani kan tsautsayi, ya bayyana cewa albasjin ya kama Naira miliyan 109.

Ya ce hakika sun yi bakin ciki bisa tsautsayin da ya auka wa al’ummar garin na Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi, kuma majalisar ta sha alwashin yin bincike domin gano musabbabin abin da ya faru.


Gwamna Uba Sani a jawabinsa ya mika godidyarsa ga dukkan ’yan majalisar da suka jajanta masa, inda ya bukaci su tabbatar da Hakimin Yan Tudun Biri ya fito kunya ta hanyar yi musu adalci.

Ya kumu nuna rashin jin dadinsa bisa yadda wasu ke neman sanya rigar addini ko kabilanci a kan abin da ya faru, inda ya ce abin ba haka yake ba.
(AMINIYA)

Tuesday, 5 December 2023

Hajj 2014 : Hukumar NAHCON Ta Kafa Kwamitin Bitar Ka'idojin Samar Da Abinci Da Gidaje.

Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON ta kaddamar da wani kwamiti da zai yi nazari kan wasu sharuddan da suka shafi masauki da abinci don samar da ingantacciyar hidima a lokacin aikin Hajjin 2024.

A sanarwar da Mataimakin daraktan yada labarai da dab'i na Hukumar Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace da yake jawabi a wurin taron, mai rikon Shugabancin Hukumar,  Malam Jalal Ahmad Arabi OON, fwc, ya bayyana cewa sake duba ka’idojin da ake da su za su taimaka wajen inganta ayyukan masu ba da hidima wanda hakan zai amfanar da Alhazan Najeriya.

A cewarsa, kundin tsarin gudanarwar kwamitin ba sabon sabon abu ba ne, amma wata hanya ce kawai ta yin la'akari da tsarin da ake da shi don samar da kyakkyawan sakamako.

“Abin da muke yi yanzu ba wai sabon abu  ba ne kawai don inganta yadda muke yin abubuwa. Kamar yadda yake faruwa a wasu sassa na duniya, muna bukatar mu kasance da ƙwazo. Kamar yadda al'ada ce ta duniya, dole ne mu inganta ta hanyoyinmu, don dacewa da mafi kyawun ayyuka na duniya," in ji shi.

Shugaban ya kuma bukaci kwamitin da ya tunkari wannan aiki da hankali da sanin ya kamata domin rahoton nasu zai yi matukar tasiri wajen yadda hukumar za ta aiwatar da ayyukan na bana.
Wuraren masauki da ayyukan samar da abinci a Saudi Arabia.

“A matsayinku na ƙwararrun ma’aikata, ba ni da tantama cewa za ku yi aikin da cikakkiyar gaskiya. Haka nan kuna da damar fadada fiye da yadda ake tunani, ta yadda duk shawarwarin da kuka bayar za su wadatar da iliminmu da kuma ci gaban Hukumar."

Da yake jawabi a madadin ‘yan kwamitin, Dakta Aliyu Tanko, ya gode wa shugaban bisa wannan damar da aka ba su na yin hidima. Ya bayyana cewa duk da cewa aikin yana da wuyar gaske amma ya bayyana fata da kwarin gwiwa ga ’yan Kwamitin na gudanar da aikin ta hanyoyin da suka dace, yana mai jaddada alakar da ke tsakanin aikin da sakamakon aikin Hajjin 2024.
“Aiki ne mai ban tsoro, ko shakka babu, domin duk abin da muka yi zai yi tasiri ga sakamakon aikin Hajjin 2024 ko dai ko dai ko dai. Amma addu’armu ita ce rahotonmu ya ba da sakamako mai kyau.”


Sunday, 3 December 2023

Yanzu-Yanzu: Ganduje ya sake nada Aminu Hikima sabon mukami a matakin kasa

A cikin sanarwar da Aminu Dahiru Ahmed ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce, wannan shi ne karo na hudu da Baba Ganduje ya nada ni. A lokacinsa na farko a matsayin gwamnan jihar Kano, ya nada ni babban mai taimaka masa na musammam kan harkokin daukar hoto. Haka kuma a wa’adinsa na biyu ya sake nada ni a Wannan matsayi.
 
Lokacin da ya bar ofis bayan shekaru takwas, ya nada ni mai daukar hotonsa na kashin kai. Nadin na baya-bayan nan shi ne na hudu.
 
Aminu Dahiru yace Baba Ganduje ya yi min abin da uba kawai zai yi wa dansa. Ya dauki nauyin karatuna da sauran abubuwa da yawa. "Wacce irin ni'imomin Ubangijinku kuke karyatawa"?

A matsayina na mai daukar hotonsa, ina da abubuwa da yawa da zan ce game da Baba Ganduje. Mai daukar hoto yana aiki tare da maigidansa. Ni ma na yi aiki tare da Baba Ganduje tsawon wadannan shekaru. Ina shaidawa tsohon gwamnan yana da riko da addini, mai tausasawa, mai kirki, mai yarda da mutuntawa har da wadanda ke karkashinsa. Kasancewara da Baba Ganduje ya kawo min sauyi ta fuskoki da dama.
 
Bangaren addini na Baba Ganduje yana da ban sha'awa. Ku yi aiki da Baba Ganduje, tabbas za ku samu yin koyi da  al'adar yin addu'o'in ku a kan lokaci, kuma ku yi ayyukanku na addini cikin aminci.
 
Baba Ganduje ya shahara wajen gina masallatai, makarantun Islamiyya, shirya gasar karatun Alkur’ani da daukar nauyinsu da musulunta. Ganduje ya zuba jari mai yawa ga marasa galihu.
 
Mataimakin na musammam ga Shugaban jam'iyyar APC ta Kasa, ya ci gaba da cewa, A siyasance Baba Ganduje shi ne ainihin ma’anar dan siyasa. Shi ne gwanin da ke bayyana siyasar zamani. Abin sha'awa Baba Ganduje yana yafiya don Allah. Yana ramuwar gayya ne kawai akan cin zarafin da aka yi masa a siyasance.
 
Ta fuskar karfafawa mutane, Aminu yace Ganduje mai baiwa ne ajin farko, wanda yake yi a boye. Zai ba ku, ya sake ba ku kuma ya tambaye ku kada ku gaya wa kowa. Wannan mai bayarwa ne na gaske.
 
Wadannan kyawawan halaye da na lissafo su a sama sun fi su Baba Ganduje da Allah Ta’ala ya karawa rayuwa lafiya, arziki, iyali da mulki. Siffofin guda ɗaya suna zama kagara tsakaninsa da masu zaginsa.
 
Allah Ta'ala Ya ci gaba da kasancewa tare da shi, Ya kuma kare shi daga dukkan sharrin masu makirci. Amin.

Na gode Baba!

Yanzu-Yanzu: Zulum ya amince da nadin Mohammed Dawule a matsayin mai rikon Hukumar Alhazai ta Jahar Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya amince da nadin Mohammed Dawule Maino a matsayin mukaddashin sakataren hukumar jin dadin alhazai ta jihar Borno.

An bayyana nadin ne a ranar Lahadin da ta gabata a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Borno, Hon. Bukar Tijjani.

Sakataren gwamnatin jihar ya kara da cewa nadin wanda ya fara aiki nan take, ya dogara ne akan cancanta da kuma bayanan shekarun baya a aikin gwamnati.

Har zuwa lokacin da Dawule ya nada shi mamba ne a sabuwar Hukumar Ilimi ta Larabci da Sangaya ta Jihar Borno (BOSASEB. Kafin nan, Dawule ya yi aiki a Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Borno tsakanin 2015 zuwa 2022.

Ya kuma yi aiki a Makarantar Sakandare ta islamiyya da ke Maiduguri da Kwalejin Gwamnati da ke Maiduguri da kuma Makarantar Alkur’ani ta Model da ke Konduga.

An haifi Mista Dawule mai shekaru 50 a duniya a karamar hukumar Kaga da ke arewacin jihar Borno.

Gwamna Zulum ya taya Mohammed Dawule Maino murna sannan ya ce yana fatan ci gaba da yi masa hidima tare da nagartar al’ummar jihar Borno.

Insight Northeast 

Wednesday, 29 November 2023

Hajj2024: NAHCON Ta Ja Hankalin Hukumar Kula Da Filayen Jiragen Kan Samar Da Kayayyakin Da Suka Wajaba

Hukumar Alhazai ta kasa ta hori hukumar dake lura da filayen jiragen sama ta kasa, da ta gaggauta samar da dukkanin kayayyakin da suka waja a bangare tashin alhazai da nufin gudanar da jigilar alhazan na wannan shekarar cikin nasara

A sanarwar da mataimakin Daraktan yada labarai da dab’I na hukumar , Mousa UIbandawaki ya sanyawa hannu, yace Mai rikon mukamin shugabancin hukumar, Malam Jalal Ahmed Arabi, shi ne yayi wannan kiran lokacin da wakilin hukumar na bangaren aikin Haji suka kai masa ziyarar ban girma a Abuja

Ya bayyana cewa samar da kayayyakin da suka wajaba a bangaren tashin alhazan dake fadin kasar nan zai taimaka matuka gaya wajen samun nasarar aikin jigilar alhazan

‘’Ku manyan abokan hula ne wajen gudanar da aikin Haji. Koda yake akwai wasu abubuwa da ake la’akari dasu yayin tashin alhazai kuma muna sa ran zaku sanar mana yanayin da filiyen jiragen saman da ake amfani dasu waje n tashin alhazai suke ciki’’

Ya bayyana cewa kwamitin ya kamata yay duba da lokaci domin saboda lokacin da suke da shi kadan ne wajen gudanar da aikinsu, duba da wa’adin da kasar Saudia ta bayar ga dukkanin kasashe wajen kamala shirinsu na aikin Haji da wuri

Tunda farko da yalke nasa jawabin, jagoran tawagar, wanda kuma ya kasance daraktan kula da ayyukan filin jiragen sama na hukumar, Kaftin Muktar Yusuf Muye, ya bayyana cewa hukumar ta shirin aikin shekara na Hajin 2024 tun watanni biyu da suka gabata domin samun nasarar gudanar da shi

Ya bayar da tabbacin cewa zasu kamala aikin kafin fara jigilar alhazai a dukkanin wuraren tashin alhazai dake filayen jiragen sama na fadin kasar nan

A saboda haka sai Kaftin Muye yayi kira ga NAHCON da ta ja hankalin kamfanoni masu zaman kansu dake jigilar alhazai dasu bayar da hadin kai ga tsarin aikin jigilar alhazansu ta bangaren tashi zuwa kasa da kasa a maimakon banagren tashin alhazai domin hakan na hana hukumar samun kudaden shiga masu muhimmanci wanda ya kamata su samu don samar da muhimman kayan inganta rayuwa a filayen jiragen

Daga nan sai ya bawa hukumar tabbacin aniyarsu wajen gudanar da aikin yadda ya kamata don alhazan Najeriya su samu damar guanar da aikin Hajin 2024 ba tare da wata matsala ba

Bayan Shekara Uku, an sake bude Kasuwar Bacci a Kaduna

Bayan shafe tsawon shekara uku ana gyaran Kasuwar Barci da ke Tudun Wada a Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, gwamnatin jihar ta sake bude kasuwar.

Ana iya tuna cewa, tsohon gwamnan jihar, Nasiru El-Rufa’i ne ya rushe kasuwar domin zamanantar da ita.

Sai dai wannan yunƙuri ya fuskanci kalubale, inda ‘yan kasuwar da dama da suka rasa shaguna da jari ke korafin kudin hayar shago da suka ce ya gagare su.

Kan haka ne Shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Kabiru Yakubu Jarimi, ya shawarci tsofaffin ’yan kasuwar da su nemi ba’asin shagunansu.

Shugaban wanda ya samu wakilcin Sakataren karamar hukumar, Abdulrahman Yahaya, ya shawarci ‘yan kasuwar da su yi watsi da shawarwarin masu hana su komawa kasuwar.

Ya ce dole ne su koma su nemi hakkin shagunansu tun da sun kasance suna da shaguna a baya a cikin kasuwar.

Aminiya


Tuesday, 28 November 2023

Abin Da Ya Kawo Cikas A Sulhun ECOWAS Da Sojin Nijar — Yusuf Tuggar

Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya ce sun yi tayin tattaunawa domin kawo ƙarshen tankiyar da ke tsakanin Ƙungiyar Raya Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) da sojojin da suka kifar da Shugaban Nijar Mohammed Bazoum, amma hakan bai yiwu ba, don kuwa shugabannin sojojin sun ƙi amincewa da yunƙurin.

Ambasada Tuggar ya faɗi hakan ne a wata hirarsa da BBC, yana mai cewa duk wata magana da ta shafi a saki Shugaba Bazoum, sojin ba su amince da ita ba.

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda 2 a Imo
Abdul Amart ya siya wa iyalan Aminu S. Bono gida
“Sun ce kar ma a yi wannan maganar, kar ma a sa shi cikin sharuɗɗan yin sulhu,” in ji Yusuf Tuggar.

Ya bayyana cewa babu ta yadda za a iya samun sulhu a wannan yanayi.

“Za su ci gaba da rike shi kenan ya yi zaman dindindin a kulle?”


Ministan ya ce sojojin da suka yi juyin mulki ne suka janyo wa Nijar takunkumin da ECOWAS ta ƙaƙaba mata, da kuma shiga halin da take ciki.

Ya ce abin da suke buƙata shi ne a saki Shugaba Bazoum.

“Muna son sojojin su saki Bazoum ya fita, a kai shi wata ƙasa daban. Ba maganar dawo da shi kan mulki ake yi ba,” in ji ministan.


Ya ƙara da cewa, duk wani yunƙuri da suka yi, sojojin sun ƙi ba da haɗin-kai ta kowanne yanayi, inda suka ce ba sa son a yi maganar ma kwata-kwata.

“Ta yaya za a yi sulhu a haka, mene ne sojojin za su yi saboda in ana son yin sulhu tsakanin mutane, gefe ɗaya zai ce ya haƙura da abu kaza, ɗaya gefen ma ya ce haka.

“To su kwata-kwata cewa suka yi, sai dai a yi musu abin da suke so,” in ji Tuggar.

Ya ce ECOWAS ba ta da matsala da ƴan Nijar kuma ba ta jin daɗin halin da suke ciki.

Ya ƙara da cewa matsalarsu ita ce sojojin da suka kama Shugaba Bazoum suka riƙe, duk da yake suna ganin akwai hanya mai sauƙi ta warware rikicin.

Ministan harkokin wajen Najeriyar ya ce dole ne idan mutane suka yi ba daidai ba a tsawatar musu.

A cewarsa, sojojin ma ba yadda suka iya da junansu don kuwa, kowa na ƙoƙarin samun ƙarfin iko a Nijar, inda a gefe guda suka bar ƴan ta’adda na can suna cin karensu babu babbaka.

Watanni huɗu bayan kakaba wa jamhuriyar Nijar takunkumi da ƙungiyar ECOWAS ta yi, sakamakon juyin mulkin sojoji, har yanzu ƴan ƙasar na ci gaba da ɗanɗana kuɗa da rayuwar ƙunci.

Farashin kayan masarufi ya yi tashin gwauron zabi, saboda rufe iyakar ƙasar da Najeriya ta yi, da kuma yanke hulɗar kasuwanci da ƙasashen ECOWAS suka yi da Nijar.

(AMINIYA)

Monday, 27 November 2023

Kofa ya shirya taron addu'a na musammam ga Tinubu, Kwankwaso da Gwamna Abba Kabir Yusuf

...Ya ce har yanzu ƙofar NNPP a buɗe take don yin ƙawance da APC da sauran jam’iyyu

Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kiru da Bebeji, Kano, a yau ya tara malamai 1,000 a garinsa na Kofa a Bebeji, Kano, domin addu’a ta musamman ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da kasar baki daya, Jagoran jam’iyyar NNPP da Ɗarikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, PhD, FNSE da kuma neman nasara ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf a Kotun Ƙoli, da kuma addu’ar neman taimakon Allah ga ɗan majalisar. 


A sanarwar da hadimin dan majalisar kan harkokin yada yada labarai, Sani Ibrahim Paki ya sanyawa hannu, yace yayin taron, malaman sun sauke Alƙur’ani sau 1,101, sannan suka yi addu’o’i na musamman.

A taƙaitaccen jawabin da ya gabatar a wajen taron, Hon. Jibrin ya ce alaƙarsa da Shugaba Tinubu ba ɓoyayya ba ce. Ya kuma ce Kwankwaso ne maigidanshi, sannan zai ci gaba da iya ƙoƙarinsa wajen ganin an samu kyakkyawar alaƙa a tsakanin Tinubun da Kwankwaso.
Jibrin ya kuma ce NNPP jam’iyya ce mai farin jini kuma har yanzu kofarta a buɗe take domin yin aiki tare, ƙawance da kuma haɗaka da APC, har ma da PDP da LP, da ma duk jam’iyyar da ta nuna sha’awar yin hakan, matukar za ta yi haka ne don amfanin ’yan Najeriya.
Ɗan majalisar mai hawa hudu ya kuma yi alkawarin yin amfani da gogewarsa da sanin mutane wajen tattaunawa da masu faɗa-a-ji a siyasar Kano, domin ganin an magance duk wata matsala da za ta iya magantuwa sannan a kawar da duk wata fargaba da ake da ita a jihar a yanzu kan shari’ar kujerar Gwamnan Jihar.
Kazalika, bayan kammala taron addu’ar, kamar yadda ya saba, Hon. Jibrin ya kuma karɓi baƙuncin ɗaliban firamare 5,000 daga faɗin mazaɓarsa, inda ya raba musu kayayyakin karatu sannan ya yi musu albishir ɗin nagartattun shirye-shirye da gwamnatin jiha da ta tarayya suke yi musu don bunƙasa ilimi, musamman a fannin samar da ilimi kyauta da kuma shirin ciyar da ’yan makaranta. 


Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada Abdullahi Musa matsayin shugaban ma'aikata

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma'aikatan gwamnati.

A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, yace nadin ya biyo bayan murabus din da tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Bala Mni ya yi na radin kansa wanda gwamnatin yanzu ta rike tun daga kafuwarta a watan Mayu, 2023.

Kwararren ma’aikacin gwamnati wanda ya yi aiki a ma’aikatu da ma’aikatu da hukumomi daban-daban a Kano sama da shekaru talatin, sabon shugaban ma’aikata ya fito ne daga karamar hukumar Kiru.

Abdullahi Musa ya rike mukamin babban sakatare na gidan gwamnatin Kano, daraktan harkokin kansiloli, Admin da Janar aiyuka na ofishin majalisar ministoci, ma’aikatar ayyuka na musamman, da kuma Servicom Directorate.

Ya kammala karatunsa na Digiri a fannin Dangantaka tsakanin kasa da kasa daga babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma ta samu digirin digirgir a fannin manufofin gwamnati da gudanarwa a jami’ar Bayero ta Kano da kuma wani digiri na biyu a fannin dabarun tsare-tsare da tsaro daga Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA), Kaduna.

Gwamna Abba Kabir ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan jihar da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa a cikin dokokin da suka shafi aikin gwamnati.


Thursday, 23 November 2023

Hukumar Alhazai Ta Kano Ta Bukaci Jami’anta Na Kananan hukumomi Da Su Gaggauta Siyar Da Kujerun Aikin Hajji

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, ya jaddada bukatar daukar matakin gaggawa na jami’an Hukumar alhazai na kananan hukumomi domin ganin an siyar da kujerun aikin Hajji a kan lokaci.

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Darakta Janar din yayi jawabin ga mahalarta taron a ranar Alhamis a taron bita na yini daya da hukumar ta shirya a sansanin ‘yan yawon bude ido na jiha, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya bukaci jami’an su kara zage damtse wajen siyar da dukkanin kujerun aikin Hajji da aka ware daga kananan hukumomi daban-daban.
Da yake karin haske game da lamarin, ya jaddada wajabcin karbar kudaden ajiya 4.500,000 daga maniyyatan da suka nufa a karshen wata mai zuwa, musamman nan da ranar 25 ga Disamba, 2023.

Bugu da kari, Alhaji Laminu Danbappa ya bayyana muhimman bayanai, inda ya bayyana cewa Saudiyya na shirin kammala bayar da bizar kwana 50 kafin Arafat a lokacin aikin Hajjin bana.
Hukumar ta nuna jin dadin ta ga hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki wajen gudanar da aikin hajji cikin kwanciyar hankali tare da hasashen kokarin da jami’an cibiyar alhazai na kananan hukumomi ke yi wajen cimma manufofin da aka ware musu.

A nasa bangaren, Daraktan ayyukan Hajji, Alhaji Kabiru Muhd ​​Panda ya bukace su da su mai da hankali sosai kan abubuwan da aka koyar dasu yayin taron.
Alhaji Kabiru Panda ya mika godiyarsa ga gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusif bisa jajircewar da ta yi na aikin Hajji.



           

NAHCON Ta Kaddamar Da Kwamitin Da Dai Zai Sake Duba Ayyukan Kwamitin Tawagar Likitoci Masu Kula Da Lafiyar Alhazai

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON a kokarinta na inganta gaskiya da kuma sake fasalin ayyukan tawagar likitoci masu kula da lafiyar alhazai ta kasa ta kaddamar da wani kwamiti mai mambobi 15 domin duba yadda tawagar zata gudanar da aikin Hajjin 2024.
;
A sanarwar da Mataimakin daraktan yada yada labarai na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace da yake jawabi yayin taron da aka gudanar a dakin taro na hukumar, Mai rikon Shugabancin Hukumar, Malam Jalal Ahmad Arabi, OON, fwc ya ce wasu daga cikin hanyoyin da tsarin sun zama na zamani da kuma wadanda ba su da tushe.

“Tawagar Likitoci ta kasa na da matukar muhimmanci wajen gudanar da ayyukan Hajji. Yana da matukar tayar da hankali cewa wasu daga cikin tsarinsa da tsarinsa suna buƙatar yin la'akari da su, idan dole ne mu sami kyakkyawan sakamako. Muna buƙatar shigar da sabbin ra'ayoyi ta yadda ake aiwatar da ayyukanta yayin da wasu daga cikin tsarinsa da  suka zama tsofaffi"
;
“Kamar yadda yake tare da duk ƙoƙarin ɗan adam, tawagar ta fuskanci ƙalubale masu yawa. Saboda haka, muna bukatar mu yi tunani a waje da akwatin kuma mu bincika wasu hanyoyi. Ta hanyar ban sha'awa, amma ita ce kawai hanyar da za mu iya canza ayyukan su. "

Shugaba wanda ya nuna amincewarsa ga mambobin kwamitin, ya shawarce su da su kasance masu sassauƙa kuma su bi ƙa'idodin / jagororin da suka gabata. 

"A cikin yin la'akari da ƙa'idodin, da fatan za a yi la'akari da ƙa'idodin ƙa'idodin don mu sami sakamako mafi girma. Tare da gwanintar ku, baya da halin ku; kuma kasancewar ka tabbatar da kanka a baya, ana sa ran ka da yawa kuma na yi imanin ba za ku bamu kunya ba,” inji shi.

Da yake mayar da jawabi, shugaban kwamitin, Dokta Saidu Ahmed Dumbulwa ya bayyana jin dadinsa da nadin da aka yi musu, ya kuma ba da tabbacin cewa tawagar za ta samar da ingantattun tsare-tsare masu inganci da sauki wadanda za su tabbatar da an yi wa alhazan Najeriya ayyuka Wadanda zasu gamsu.

Kwamitin wanda ke da makonni biyu don gabatar da shawarwarin shi ne don kimanta tasiri tare da gano gazawar a cikin Jagororin tawagar Likitoci ta Kasa na yanzu; don yin nazari da tantance ayyukan masu ruwa da tsaki a Najeriya da kuma mahimmin gudunmawar da suke bayarwa a cikin ayyukan tawagar likitocin ƙasa da sauransu a matsayin wani ɓangare
 

Najeriya Za Ta Fara Fitar Da Tataccen Mai Kasar Waje A 2024 —NNPCL

Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) Mele Kyari ya ce Najeriya za ta zama kasa mai fitar da tataccen man fetur da dangoginsa zuwa kasashen waje a shekarar 2024 mai kamawa.

Mele Kyari ya kuma ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa cikin watanni uku masu zuwa ba za a samu karancin man fetur ba, kamar yadda ake gani a lokacin bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

“Ina tabbatar wa shugabannin majalisa ba za a fuskanci karancin mai ba.


“Za ku ji ana ta yada labarin layuka a gidajen mai, amma ba gaskiya ba ne,” in ji Mele Kyari.


Hukuncin da muka zartar na korar Gwamnan Kano na nan daram – Kotu
Magoya bayan NNPP sun yi zanga-zanga kan hukuncin kotu a Kano
Ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci shugabannin majalisar dattawa.

Ya kara da cewa NNPC zai gyara matatar mai ta garin Fatakwal a wata mai kamawa, sannnan matatar mai ta Warri ta biyo baya a farkon 2024.

Haka zalika, ya yi hasashen NNPCL zai samu ribar da ta kai triliyan biyu a shekarar 2023 da ke dab da karewa.

Kyari ya shaida wa shugabannin majalisar dattawa cewa amincewa da sabuwar dokar man fetur, ta saka man ya wadata kuma a farashi mai sauki a kasar nan.


Da yake jawabi kan matsalar fasa bututu da satar mai, Kyari ya ce jami’an tsaro na musamman da ke yaki da bata-garin, sun taimaka musu wajen kwato gangunan danyen mai na kusan naira miliyan biyu.

Da yake jawabi, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya gode wa kamfanin man bisa hadin kai da ya bai wa Gwamnatin Tarayya wajen cire tallafin man fetur.

(AMINIYA)

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Gwamna Abdullahi Sule Na Jahar Nassarawa

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule. 

Kotun daukaka kara ta kuma yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Nasarawa ta yanke a ranar 2 ga watan Oktoba da ta kori Sule na jam’iyyar APC tare da bayyana David Ombugadu, dan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna. 

Da yake yanke hukunci, kwamitin mutum uku ya ce kotun ta yi kuskure wajen yanke hukuncin cewa Gwamna Sule bai samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba. 

Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 


Tuesday, 21 November 2023

Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Kano Ta Jaddada Bukatar Biyan Kudin Aikin Hajji A Kan Lokaci

Daraktan janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano Alh Laminu Rabi’u Danbappa ya jaddada muhimmancin hada kai da Limamai Juma’a. Wannan hadin gwiwar na da nufin fadakar da alhazai kan wajibcin gaggauta biyan kudaden ajiya na Hajji don tabbatar da cimma manufofin da aka sanya a gaba. 

A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace taron da aka gudanar yau a dakin taro na sansanin yawon bude ido na jiha Alh Laminu Rabi'u Danbappa ya bayyana kudirinsa na yin aiki kafada da kafada da limaman Juma'a na dukkan kananan hukumomin. 
Hanyar haɗin kan za ta taimaka wajen isar da sako  ga mahajjata masu niyya, tare da buƙace su da su cika  ajiyar kuɗin aikin Hajji cikin gaggawa. 

Babban daraktan ya jaddada muhimmancin hadin kai da hadin kai wajen samun nasarar aikin Hajji ba tare da wata matsala ba. 

Ya kuma bukaci limaman Juma’a da su kara himma tare da al’ummominsu domin yada muhimman bayanai dangane da muhimmancin riko da wa’adin biyan Kudin aikin Hajji da aka kayyade. 

Darakta Janar din ya kara da cewa wannan kokarin na hadin gwiwa an shirya shi ne don inganta hadin kai, tare da tabbatar da cewa an gudanar da dukkan abubuwan da suka shafi dabaru da gudanarwa na aikin hajji yadda ya kamata. 

A nasa jawabin shugaban yan hukumar gudanarwar na hukumar, Alh, Yusif Lawan ya shawarci manyan limaman da su isar da wannan sako ga sauran limamai a yankunansu. 
Da yake mayar da jawabi, Shugaban kungiyar limaman Kano, Sheikh Muhd ​​Nasir Adam, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi la’akari da tallafin dala dalar Amurka ga maniyyata. 
Sheikh Nasiru Adam yayi alkawarin bayar da cikakken hadin kai domin cimma manufofin da aka sa gaba. 


Saturday, 18 November 2023

Sojoji Sun Kutsa Ofishin EFCC Dake Kuduna Domin Kubutar Da Abokan Aikinsu

Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami'an sojin saman ƙasar suka kutsa ofishinta da ke Kaduna domin ƙwato 'yan uwansu da hukumar ta tare bisa zargin 'karya dokar aikin tsaro'.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun jami'ain hulɗa da jama'a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba jami'an EFCC sun kama wasu mutum biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuɗi ta intanet a unguwar Barnawa da ke birnin Kaduna

Hukumar ta ce ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida - da suka haɗar da sojoji huɗu da ɗaliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu - waɗanda ke wurin a lokaci da aka kama waɗanda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna ƙawanya da nufin tilasta sakin mutanen.

''Daga nan ne kuma aka kama su tare da tsare su a ofishin hukumar, bisa zargin karya dokar aiki tsaro", kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

A yayin da ake tare da mutanen hukumar EFCC ta ce ta tuntuɓi rundunar sojin sama ta ƙasa inda hukumomin biyu ke tattanawa domin warware lamarin.

Dele Oyewale ya ce a ranar Juma'a wasu jami'an sojin sama sun dirar wa ofishin EFCCn da ke Kaduna a cikin shirin faɗa, don tilasta sakin abokan aikin nasu.

"Hukumar EFCC ta yi aiki cikin nutsuwa, inda ta ci gaba da tattaunawa da jagororin rundunar sojin saman, kuma daga ƙarshe aka cimma matsayar sakin sojojin bayan an ɗauki bayansu", kamar yadda mai magana da yawun EFCCn ya bayyana.
(BBC HAUSA)

Hukuncin Kotu: Sakon Dr Nasiru Yusuf Gawuna Ga Al'umar Kano

Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki daya tabbatar da nasararmu a yau a kotun daukaka kara ta zaben gwamna.

Ina so in gode wa kotun daukaka kara saboda hukuncin da ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar da muka samu a kotun sauraron kararrakin zabe.

Tabbatar da gaskiyar da kotun daukaka kara ta yi tabbas zai karfafa dimokradiyya.

Ina so in yi amfani da damar in yaba wa alkalan kotunan zabe da na kotun daukaka kara da suka tsaya kan gaskiya don ganin an yi adalci.

Dukkan hukunce-hukuncen biyu sun sake tabbatar da cewa bangaren shari'a shine fata na karshe na talaka.

Wannan nasara ce ga daukacin al’ummar jihar nan da mazauna jihar, don haka ina neman goyon bayan kowa ba tare da la’akari da jam’iyya ba don mu hada kai da ni da abokina Alh.Murtala Sule Garo don ci gaban Kano.

Dole ne in gode wa jagoranmu mai kaunarmu, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Dr.Abdullahi Umar Ganduje, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sen. Barau Jibrin da Ministoci biyu daga Jihar Kano bisa goyon bayan da suka ba mu.

Ina kuma godiya ga shugaban jam'iyyar APC na jiha Alh.Abdullahi Abbas, shuwagabannin jam'iyyar, 'yan majalisun tarayya da na jiha, da shugabannin kananan hukumomi da jiga-jigan jam'iyyar tun daga mataki zuwa jiha.

Ina kara yabawa dukkan Malamai, Al'umman Kasuwanci, Matasa da Kungiyoyin Mata bisa hadin kai da Addu'o'i.

Manufarmu ita ce ci gaba da ci gaba ta hanyar inganta rayuwar mazauna jihar Kano da jama'ar jihar.

Ina kira ga mazauna jihar da jama'ar jihar da su kwantar da hankula su ci gaba da bin doka da oda.

Dr. Nasiru Yusuf Gawuna
Tsohon Mataimakin Gwamna kuma Dan Takarar Gwamna na APC
18 ga Nuwamba, 2023.

Yanzu-yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir Zai Daukaka Kara Zuwa Kotun Koli


...... Ya Bayyana Hukuncin Daukaka, Rashin Adalci

Bayan nazari na tsanaki da masu ruwa da tsaki, gwamnan jihar Kano da  NNPP sun yanke shawarar tunkarar kotun koli kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke jiya a Abuja.

A sanarwar da babban sakataren yada yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, yace Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a daren Juma’a a wani jawabi na musamman da aka yi wa mutanen Kano a matsayin martani ga hukuncin kotun daukaka kara da aka bayyana a matsayin rashin adalci.

“Ina so in sanar da mutanen Kano nagari kuma hakika ‘yan Najeriya cewa bisa ga amincewar masu ruwa da tsakinmu, mun umurci lauyoyin mu da su fara daukaka karar wannan hukunci a kotun kolin Najeriya, muna da kwarin gwiwar cewa babbar kotun koli ta Najeriya. Kotu da yardar Allah SWT za ta kawar da wadannan kura-kurai na shari’a da kotunan daukaka kara da kotunan daukaka kara ke yi, sannan ta sake tabbatar mana da aikin da mutanen jihar Kano nagari suka ba mu”. Inji Gwamna.

Ya yi amfani da damar wajen yin kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na halal domin gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin su a jihar a matsayin babban nauyi.

Alhaji Abba Kabir ya tabbatar da cewa koma bayan da aka samu na wucin gadi ba zai sa gwamnatin sa ta jajirce wajen ci gaba da ayyuka da shirye-shirye masu yabo da nufin dawo da martabar jihar da aka rasa ba. A cewar Gwamnan, a maimakon haka, zai kara fito da wani shiri na samar da dimokuradiyya ga ‘yan kasa da mazauna jihar Kano.

Ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da sauran ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su ci gaba da yi wa Kano addu’ar samun rahamar Allah da kariyarsa domin ceto jihar daga zaluncin ‘yan barna da ke neman yin awon gaba da mulki ta kofar baya da kuma dawo da jihar. zuwa duhu zamanai.


Wednesday, 15 November 2023

Labari da dumiduminsa: Kungiyar Kwadago ta janye yajin aikin da ta fara gudanarwa

Kungiyar Kwadagon ta kasa ta Janye yajin aikin ne bayan zaman tattaunawar da mai bawa Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu

Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Monday, 13 November 2023

Kotu Ta Dage Shari'ar Rarara Kan Sukar Buhari

Wata Kotun Majistiri da ke zamanta a Lafiya, babban birnin Jihar Nassarawa, ta dage sauraron kara da aka shigar da mawakin siyasa, Dauda Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, kan zarginsa da neman tunzura al’umma da kuma tayar da hankali.

Karar wanda wani mazaunin garin Mararraba da ke makotaka da Abuja mai suna Muhammad Sani Zangina ya shigar, ya danganta shi ne da wani jawabin taron ’yan jarida da ya ce mawakin ya shirya a Abuja, inda ya bayyana nadamar goyon bayansa ga tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tare da zarginsa da wargaza kasar kafin mika ta ga Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu.

An sa zare tsakanin Rarara da mutanen Buhari
Sabuwar wakar Rarara ta sake yamutsa hazo
A takardar karar wadda wakilinmu ya samu gani, lauyan mai shigar da karar, Barista Muhammad Barde Abdullahi ya gabatar, ya ce zargin da ake yi wa Rararan da aikatawa, ya saba da doka ta 114 a Kundin Shari’a na penal code.

Sai dai a yayin zaman fara sauraron shari’ar a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba, an sanar da kotun cewa wanda ake zargin bai halarci zaman kotun ba.


Jami’in kotun da aka baiwa takardar gayyata don mikata ga wanda ake zargi, ya shaida wa kotun cewa dogaran mawakin ba su ba shi damar kaiwa gare shi ba, a lokacin da ya yi yunkurin hakan a mazauninsa da ke Abuja, bisa zargin suna cika umarnin uban gidansu ne.

Mai shari’a Maryam Nadabo ta amince da bukatar lauyan mai shigar da karar ta a gabatar da takardar gayyatar ta hanyar likata a jikin gidan mawakin, sannan ta dage ranar fara sauraron shari’ar zuwa 4 ga watan Disamba da ke tafe.

(AMINIYA)

Kungiyar Kwadago Za Ta Fara Yajin Aikin Sai Baba Ta Gani Daga Gobe Talata

Kungiyar Kwadago ta Najeriya da kungiyar ‘yan kasuwa ta Najeriya sun umurci mambobin kungiyar da su shiga yajin aikin gama gari daga tsakar daren ranar 14 ga Nuwamba, 2023.

Shugaban kungiyar ta TUC, Festus Osifo ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Osifo ya ce yajin aikin zai ci gaba da kasancewa har sai “gwamnati a dukkan matakai sun farga da alhakin da ya rataya a wuyansu.”

Har ila yau yajin aikin na zanga-zangar ne don nuna rashin amincewa da yadda aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero, da wasu shugabannin majalisar suka yi a Owerri, jihar Imo, a ranar 1 ga watan Nuwamba, da kuma matsalolin da ke addabar ma’aikata a jihar Imo.

‘Yan sanda sun kama Ajaero ne gabanin wata zanga-zangar da aka yi a jihar Imo, kamar yadda shugaban yada labarai na NLC, Benson Upah ya bayyana.

Ko da yake rundunar ‘yan sandan ta musanta kama Ajaero, inda ta bayyana cewa an tsare shi ne kawai don kare kai harin, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya zargi shugaban kungiyar kwadagon da yin katsalandan a harkokin siyasar jihar
(Daily Commerce)

Abdulmumin Jibrin Kofa Ya Shirya Taron Addu'a Kan Nasarar Kotu, Ya Kuma Tallafa Wa Mutum 10,000

Dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Bebeji da Kiru, Abdulmumin Jibrin Kofa, ya shirya taro na musamman wanda ya haɗa sama da mutum 10,000 domin yin addu’o’i a garinsa na Kofa da ke Karamar Hukumar Bebeji ta Jihar Kano a ranar Lahadi 

Ɗan majalisar mai hawa huɗu ya shirya taron ne domin ya gode wa Allah saboda nasarar da ya samu a Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓe da ta Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja a kwanakin baya, da kuma raba wasu kayan tallafi ga ’yan mazabarsa.
A yayin kasaitaccen taron dai, an bayar da tallafi ga ’yan mazabar su 10,000 maza da mata. Bugu da ƙari, an ba mutanen tallafin kuɗi da kayan sanaa da motoci da kayan abinci da sutturu da kuma sauran kayan amfanin yau da kullum.
Kazalika, an yi addu’a ta musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, domin neman Allah Ya ba shi nasara a Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta Ƙoli, da sauran ’yan majalisar Kano na NNPP da suka yi nasara a kotu, da ma fatan nasara ga waɗanda ba a kai ga yanke nasu hukuncin ba. Sannan an yi wa jagoran Ɗariƙar Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, addu’ar neman Allah Ya ja kwanan sa, Ya ƙara masa lafiya da kuma biya masa bukatunsa.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...