Babu Wanda Nake Tsoro —El-Rufai Ga ‘’Yan Fadar Buhari’
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya kalubalancin ’yan fadar shugaban kasa da yake zargi da zagon kasa ga takarar Bola Tinubu a zaben shugaban kasa da ke tafe. Tun a ranar Laraba El-Rufai ya fara tayar da kura da zargin cewa akwai jami’an Fadar Shugaban Kasa da ke neman yi wa takarar Tinubu kafar ungulu. A wata hirarsa da Sashen BBC na Hausa, an ji shi yana cewa, “Na rantse babu mahalukin da nake tsoro a duk fadin kasar nan. “Don ana ganin girmn mutum ba soronsa ake ji ba; Amma idan muna girmama mutum, amma yana nuna shi ba babba ba ne, to wallahi za mu ake shi.” Ana ganin kalaman nasa kari ne a kan zargin wadanda yake zargi a fadar shugaban kasa, da ya cesuna neman tadiye inubu. BBC sun fitar da somin-tabin hirar ce kafin a fitar da shi gaba dayansa. A ranar Laraba, a waya hira da shirin Sunrise Daily na gidan alabijin na Channels ne El-Rufai ya yi zargin akwai magoya baan wadanda suka nemi takarar shugaban kasa a APC wanda Tibubu a lashe da ke fakewa da Shugaba Buhari domin ...