Posts

Showing posts with the label Gwamna Ortom

Har Yanzu Ban Taba Ganin Sabbin Takardun Naira Ba- Gwamna Ortom

Image
Gwamna Jihar Benuwe, Samuel Ortom, ya bayyana cewa duk da matsayinsa na mai rike da mafar iko amma har yanzu bai taba hada ido da sabbin takardun Naira ba. Mista Ortom ya bayyana hakan a wannan Larabar yayin da yake kira ga mahukunta da su tsawaita wa’adin amfani da tsofaffin takardun kudin kasar. Gwamnan ya bayyana damuwa dangane da karancin wa’adin amfani da tsohuwar naira da aka bai wa ’yan Najeriya, yana mai jan hankali da a yi la’akari da mazauna karkara da ba su da masaniyar abin da ke faruwa dangane da sauya wa takardun kudin fasali. Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamnan ya yi wannan koke ne a jawabinsa yayin ziyarar da Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Sarwaaun Tarka ta kai Fadar Gwamnatin Benuwe da ke birnin Makurdi. A cewarsa, ­“a matsayina na Gwamna, har yanzu ban yi ido biyu da sabbin takardun Naira ba duk da cewa kwanaki shida kacal suka rage wa’adin amfani da tsohuwar naira ya cika. “Yanzu a irin wannan yanayi ya za a karke ke nan da mazauna karkara? “Ina goyon bayan ...