Search This Blog

Showing posts with label Kwamiti. Show all posts
Showing posts with label Kwamiti. Show all posts

Tuesday, 22 September 2026

Kwanitin Yaki Da Shan Muyagun Kwayoyi Na Kano, Ya Kama Mutane Fiye Da 380, Ya Samu Samu Hukuncin Kotu Kan Mutane 230 Cikin Watanni Biyu

Rundunar hadin gwiwar hukumomi da gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin yaki da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kama mutane sama da 380 tare da samun hukuncin kotu kan mutane fiye da 230 cikin watanni biyu da fara aiki.
Shugaban rundunar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, watanni biyu bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rundunar domin daidaita matakan jihar na yaki da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, fataucin miyagun ƙwayoyi, daba da sauran laifukan da ke da alaka da shaye-shaye.
Da yake magana a wani taron manema labarai a Kano, Muhuyi ya ce rundunar ta gudanar da samame na hadin gwiwa a wuraren da ake zargin ana sayarwa da shan miyagun ƙwayoyi da kuma wasu wuraren da ake aikata laifuka, lamarin da ya kai ga kama wadanda ake zargi tare da kwato miyagun ƙwayoyi daban-daban.
Ya ce wuraren da aka gudanar da ayyukan sun hada da Race Course, Filin Idi, Filin Mahaha, Tashar Rami da Kawo, da sauran wurare a cikin birnin Kano da wajen sa.
A cewarsa, an kwato abubuwa da suka hada da Cannabis Sativa, Exol-5, Diazepam, allurar Pentazocine, Tramadol, kapsul din Pregabalin, Rubber Solution da sauran miyagun abubuwa.
Muhuyi ya ce: “Wannan ba aikin tarwatsa wuraren bane kawai. Wadannan samame sun kai ga kama mutane sama da 380 tare da kwato miyagun abubuwa iri-iri.”

Rundunar ta kuma kwato makamai da aka kera a gida, ciki har da wuka, adda, takubba da sanduna, wadanda Muhuyi ya ce wasu daga cikin masu safarar miyagun ƙwayoyi da ’yan daba ke amfani da su wajen tsoratar da jama’a da kuma bijirewa jami’an tsaro yayin kama su.
Wani babban abin damuwa da aka bayyana a taron shi ne zargin karkatar da magungunan da aka kayyade daga hanyoyin rarraba magunguna na halal zuwa amfani ba bisa ka’ida ba.

Muhuyi ya bayyana cewa rundunar ta kwace kusan kapsul din Pregabalin 870,000 daga hannun daya daga cikin manyan kamfanonin magunguna a jihar bisa zargin karkatar da su zuwa amfani ba bisa ka’ida ba.
Ya gargadi kamfanonin magunguna, manajojin pharmacy, superintendent pharmacists da sauran ma’aikatan fannin da su kara karfafa tsarin kula da magunguna tare da ba da hadin kai ga bincike.

“Ba za mu bar kowa ba idan aka same shi da laifi,” in ji shi.
Shugaban rundunar ya kuma bayyana cewa an riga an samu hukuncin kotu kan mutane sama da 230 a cikin shari’o’in da rundunar ta kai gaban kotu cikin watanni biyu.

Daga cikin shari’o’in akwai hukuncin da aka yanke wa wasu dillalan Rubber Solution, Kabiru Isa, wanda aka fi sani da Mada, da Usman Hamisu, wanda aka fi sani da Mani, bisa zargin jefa yara 43 da ba su kai shekaru ba cikin amfani da abubuwan maye.
Muhuyi ya ce yaran, wadanda ke aikin kwashe shara a kan tituna, ana zargin ana ba su Rubber Solution da wasu abubuwa masu maye maimakon a biya su yadda ya kamata.

Ya ce an ceto yaran 43 tare da yi musu gwaje-gwajen lafiya, ba su shawarwari da kuma magani, yayin da ake ci gaba da kokarin gano iyalansu.

Ya kara da cewa an riga an mayar da wasu daga cikin yaran ga iyalansu.

Rundunar ta kuma bayyana ci gaba a yakin da take yi da Daba, inda Muhuyi ya ambaci wasu daga cikin ’yan kungiyoyin daba da aka samu da laifi, ciki har da Abdullahi Ahmad, wanda aka fi sani da Horror; Abubakar Sada, wanda aka fi sani da Daburi; Abdullahi Sani, wanda aka fi sani da Sarki Ale; da Umar Aliyu.

Ya ce wasu daga cikin wadanda ake zargin sun yi amfani da kafafen sada zumunta wajen daukaka dabi’un daba, tunzura jama’a da kuma karfafa wasu su shiga ayyukan laifi.

A wani samame kuma, rundunar ta ce ta kama tare da samun hukuncin kotu kan wani mamba na wata fitacciyar kungiyar masu satar wayoyin hannu da aka fi sani da “Yan Liya”, tare da kwace wani keke mai kafa uku (tricycle) da ake zargin an yi amfani da shi wajen aikata laifin.

A cewar Muhuyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ba zai iya kirga adadin wayoyin da kungiyar ta sata ba.

Ya kuma yi zargin cewa wasu masu tricycle din da kungiyar ke amfani da su suna sane da ayyukan laifin da direbobinsu ke aikatawa, har ma suna cin gajiyar hakan ta hanyar neman karin kudin da za a ba su.

Saboda haka, Muhuyi ya gargadi masu tricycle da kada su bari a yi amfani da motocinsu wajen aikata laifuka da gangan, yana mai cewa rundunar za ta nemi kwace motocin da aka yi amfani da su wajen aikata laifuka.

Baya ga matakan hukunci, rundunar ta ce ta tura kimanin mutane 125 zuwa Cibiyar Gyaran Halayya ta Kano da ke Kiru domin samun horo da gyaran hali.

Muhuyi ya ce karuwar bukatar samun kulawar gyaran hali ta sa cibiyar Kiru ta cika, lamarin da ya sanya gwamnatin jihar samar da wata sabuwar cibiyar a Karamar Hukumar Tofa.

Ya ce za a samar da kayan aiki a sabuwar cibiyar tare da fara amfani da ita domin karbar mutanen da ke bukatar gyaran hali.

Ya kara da cewa rundunar tana tattaunawa da masu ruwa da tsaki a masana’antu domin samar da ayyukan yi da koyar da sana’o’i ga matasan da aka yi wa gyaran hali.

“Manufarmu ita ce mu kawar da matasa 10,000 daga tituna, mu yi musu gyaran hali, sannan mu koya musu sana’o’i, domin su koma cikin al’umma suna da cikakken ilimi, an gyara halayensu, kuma su zama mutanen da al’umma za ta amince da su,” in ji shi.

Muhuyi ya ce rundunar za ta ci gaba da hada matakan daukar doka da rigakafi, wayar da kan jama’a, gyaran hali da kuma sake shigar da wadanda aka gyara cikin al’umma.

Ya ce shirye-shiryen wayar da kan jama’a sun kai ga al’ummomi, makarantu, kasuwanni, cibiyoyin addini da sauran sassan jihar.

Ya danganta nasarorin farko da rundunar ta samu da hadin gwiwar hukumomin tsaro da na tabbatar da doka, wadanda suka hada da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, DSS, NSCDC, Hukumar Kwastam, Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali, KOSSAP, Hisbah, KAROTA da kungiyoyin sa-kai.

Shugaban rundunar ya kuma bukaci mazauna jihar da su rika bayar da bayanai cikin gaggawa game da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, fataucinsu da sauran ayyukan laifuka masu alaka da su, domin hukumomi su samu damar daukar matakan da suka dace.

SolaceBase ta rawaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rundunar a ranar 22 ga Yuli, 2026, a wani bangare na kokarin gwamnatin jihar na dakile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da laifukan da ke da alaka da su a fadin Kano.

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Kwanitin Yaki Da Shan Muyagun Kwayoyi Na Kano, Ya Kama Mutane Fiye Da 380, Ya Samu Samu Hukuncin Kotu Kan Mutane 230 Cikin Watanni Biyu

Rundunar hadin gwiwar hukumomi da gwamnatin Jihar Kano ta kafa domin yaki da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da fataucin miyagun ƙw...