Masu Niyyar Zuwa Aikin Hajji Mai Zuwa, Zasu Ga Tagomashi Daga Gwamnatin Abba Gida - Zulaiha Yusuf Aji
Maitamakawa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf a kan kafafen yada labarai na rediyo da talbinjin Hajiya Zulaihat Yusuf Aji, ta ce gwamnatin jihar Kano duk da sabuwa ce amma ta yi kokari mutuka, idan ka duba gwamnatin ce da ta shigo daf da za fara dibar alhazai wanda tuni wasu jihohin sun fara jigilar maniyatan, amma abun da zai baka mamaki shi ne tun a Madina a ka fara bawa alhazan Kano abinci sau uku a rana baya ga kawo motoci a debe su zuwa guraren ziyara a Madina sannan a ka kuma dauko su zuwa Mak ka. "Mun zo Makkah kuma mun je Mina, zaman Mina alhamdulillah wakiliyar sashin Hausa ta muryar Amuruka Baraka ta hira da ni kan matsalolin takari mazauna kasar Saudiya ina ganin akwai matakin da za a dauka "Tun a jirgin farko da za su fara tashi mai girma gwamna ya zo ya yi musu sallama yayi musu bakwana ya kuma ba su hakuri, duk abun da su ka gani a Mina su yi hakuri ba wannan gwamnatin ce ta tsara musu ba. Duk alhaji da ya wannan shekarar a shekara mai zuwa idan...