Sarkin Kano Ya Bukaci Gwamnati Ta Samar Da Wata Hanyar Da Al'uma Zasu Samu Saukin Rayuwa
Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakan ne lokacin da ya kai ziyarar barka da sallah gidan Gwamnatin jihar Kano a hawan Nassarawa da ya gabatar yau Lahadi a cigaba da gudanar da haye hayen sallah karama. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Naisa ya sanyawa hannu, Sarkin yace sakamako matsin rayuwa da ake fama da ita akwai bukatar Gwamnati da mawadata su tallafawa marasa shi domin samun saukin gudanar da al'amuran rayuwarsu. Ya kuma tunasar da al'uma shirin gwamnati na Kidayar al'uma da za'a gudanar a dukkanin fadin kasar nan inda ya bukaci al'uma dasu tabbatar an kidayasu a lokacin gudanar da aikin kidayar. Mai Martaba Sarkin godewa Gwamnatin jihar Kano bisa kokarinta na samar da Tsaro da Zaman lafiya inda ya godewa Malamai da limamai wajan gudanar da addu'oi domin dorewar Zaman lafiya a jihar Kano. Alhaji Aminu Ado Bayero yayi kira ga al'uma su cigaba da baiwa gwamnati goyon baya yace duk wasu aikace aikac...