A maimakon haka, majalisar ta bukaci a mayar da kudin wajen kara yawan kuษin da aka ware domin ba dalibai rancen, wanda a baya aka ware wa biliyan 10.
‘Barayin’ da suka je fashi sun ษige da satar tukwanen miya da abinci a Kalaba
Majalisa ta amince da kwarya-kwaryar kasafin kudin Tinubu na tiriliyan 2.17
Aminiya ta rawaito cewa matakin ’yan majalisar ba zai rasa nasaba da koke-koken da ’yan Najeriya suka rika yi ba tun bayan bullar labarin, inda suka ce ya zo a daidai lokacin da ’yan kasa ke korafin kuncin rayuwa.
Shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Abubakar Kabir (APC, Kano) ne ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan da kammala amincewa da kasafin a Abuja.
Ya ce daukar matakin ya zama wajibi la’akari da kudin da aka ware wa daliban a cikin kasafin ya yi kadan.
Abubakar ya kuma ce kwamitin ya kason da aka ware wa Ma’aikatar Tsaro daga Naira biliyan 476 zuwa 546 sakamakon ฦaruwar kalubalen tsaro.
Shugaban kwamitin ya kuma ce sun duba tare da amincewa da batun kara mafi ฦarancin albashin ma’aikata domin mika shi ga bangaren zartarwa.
Sai dai ya ce za su tabbatar suna sanya idanu ga bangaren zartarwa domin ganin sun yi abin da ya dace.
Amma daga bisani Fadar Shugaban Kasa ta ce jirgin ruwa ba na amfanin Tinubu ba ne, na Rundunar Sojin Ruwan Najeriya ne
(AMINIYA)