Shugaban NAHCON Ya Kai Ziyarar Neman Hadin Kai Ga Babban Limamin Legas Da Sauran Masu Ruwa Da Tsaki
A ci gaba da ziyarar tuntubar da yake yi wa masu ruwa da tsaki a fadin kasar nan, shugaban riko/shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Malam Jalal Ahmad Arabi OON, FWC, ya kai ziyarar ban girma ga babban limamin Legas, Fadilat Sheikh Sulaiman Oluwatoyin. Abou Ola, da kungiyar Ansaru Deen Society of Nigeria. Da yake jawabi a wajen taron, shugaban NAHCON ya ce ya yanke shawarar ziyartar malamin da kungiyar musulmi ne domin neman goyon bayansu da hadin kai a kokarin da hukumar ke yi na yi wa al’ummar kasa hidima musamman mahajjata. A sanarwar da Mataimakin daraktan yada labarai da dab'i na Hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, Shugabn a cewarsa, ya zama wajibi shugabannin musulmi su tashi tsaye wajen wayar da kan alhazai a wani bangare na ayyukansu na mishan kamar yadda Allah Madaukakin Sarki ya yi umarni da su. “Na zo nan ne domin in tunatar da malamanmu da shuwagabanninmu ayyukansu na addini da su taimaka wajen ilimantar da al’ummarmu, ba za mu iya yin watsi d...