Rashin tsaro: Gwamnatin Kano Tayi Alkawarin Taimakawa Gwamnatin Tarayya Akan Yaki Da Masu Ta'addanci da Satar Mutane
Gwamnatin jihar Kano ta lashi takobin marawa shirin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu baya na dakile illolin rashin tsaro da ke dagula zaman lafiya a kasar nan. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wannan alkawarin ne a ranar Juma’a a lokacin da ya karbi bakuncin ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Alhaji Muhammad Idris a ziyarar ban girma da ya kai gidan gwamnati. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya ce ya dace a hada kai da gwamnatin tsakiya domin dakile wuce gona da iri domin dawo da ci gaban kasa. Alhaji Yusuf ya yabawa shugaba Tinubu bisa yadda ya yi biyayya ga kiran da ya yi na sake bude iyakokin Najeriya da wasu kasashe, matakin da zai taimaka wajen rage wahalhalun tattalin arzikin kasar. Ya kuma bayyana ziyarar a matsayin wacce ta dace da la’akari da yadda ta ke gudanar da harkokinta da masu ruwa da tsaki ciki har da ‘yan kasuwa da suka yi alkawarin yin duk abin da ya kamata na marawa gwamnatin taray...