Bola Tinubu Ya Bar Najeriya Zuwa Turai Domin Ziyarar Aiki
A yammacin Larabar nan ne zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bar Najeriya zuwa kasashen Turai domin ziyarar aiki. A sanarwar da daya daga masu hidima masa a fannin yada labarai, Tunde Rahman ya fitar, ta ce Zai yi amfani da damar tafiya don daidaita tsare-tsare da shirye-shiryen mika mulki, da zabin manufofinsa tare da wasu manyan mataimakansa ba tare da matsananciyar wahala da damuwa ba. A yayin ziyarar, zababben shugaban kasar zai tattauna da masu zuba jari da sauran manyan abokan hulda da nufin tallata guraben zuba jari a kasar da kuma shirye-shiryen gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau na kasuwanci ta hanyar manufofi da ka'idoji. Asiwaju Tinubu na fatan gamsar da su kan shirin Najeriya na yin kasuwanci a karkashin jagorancinsa ta hanyar hadin gwiwar da za ta amfana da juna kan samar da ayyukan yi da kuma samun kwarewa. Farfado da tattalin arzikin kasar ya zama wani babban ginshiki na ajandar sabunta fata na Tinubu kuma taron na daya daga cikin k...