Posts

Showing posts with the label Sarkin Dutse

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Jigawa ya amince da nadin Sabon Sarkin Dutse

Image
Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya amince da nadin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon sarkin Dutse. Kadaura24 ta rawaito Sanarwar amincewa da nadin na dauke da sa hannun kwamishinan aiyukan na musamman na jihar Jigawa Auwalu D Sankara,wadda kuma aka rabawa manema labarai. Nadin ya biyo bayan zaben Masu Zaben Sarki na Masarautar Dutse su bakwai suka yi wa Hameem daga cikin masu neman kujerar sarautar har su su uku.  Majalisar Sarakunan Jihar Jigawa ta amince da zaben, sannan kuma nadin sa ya fara aiki daga ranar 5 ga Fabrairu, 2023.  Sabon Sarkin dai ya gaji Mahaifinsa ne Alhaji Nuhu Muhd Sanusi II wanda Allah ya yiwa rasuwa a makon daya

Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi ya Rasu

Image
Marigayi Mai Martaba Dokta Nuhu Muhammadu Sanusi shi ne basaraken gargajiya mai ajin farko (Sarki) na Dutse babban birnin jihar Jigawa a yankin Arewa maso yammacin Najeriya. Sannan kuma shi ne Shugaban Jami’ar Jihar Sakkwato. Sarki Sanusi shine jagoran masu fafutukar kare gandun daji da kuma koren halittu a fadin masarautarsa Wannan alÆ™awarin rage tasirin sauyin yanayi ne ya sa ya gina filin wasan Golf na Dutse wanda ake kyautata zaton na É—aya daga cikin mafi girma a Najeriya da ke da ciyayi masu  masu yawa da namun daji. Kafin ya hau karagar mulki, Dr. Sanusi ya samu gogewa sosai a fannin tuntubar juna a fannin noma da sarrafa sarkakkun ayyukan masana'antu a nahiyoyi. Baya ga sha'awar tafiye-tafiye, Sarki Sanusi ya gabatar da kasidu a tarurrukan karawa juna sani na kasa da kasa, kuma ya rubuta litattafai da dama, ciki har da tarihin rayuwarsa da kuma tarihin Dutse mai zurfi. A karkashin mulkinsa, Masarautar Dutse na rikidewa d zuwa samun ci gaba inda al'umar ya