Posts

Showing posts with the label Ayyukan alkhairi

Karin ayyukan alheri na nan tafe ga al'ummar Kano -- Gwamna Abba K. Yusuf

Image
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da gudanar da ayyuka da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’ummar jihar. Da yake jawabi a lokacin da yake duba ayyukan ofishin sa a cikin makonni 3 da suka gabata a yayin da aka fara taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 7 a gidan gwamnati da ke Kano, gwamnan ya ce an fara gudanar da ayyukan alheri da dama. A sanarwar da babban sakataren yada labaran Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu, Gwamnan ya bayyana cewa, a cikin wannan lokaci da gwamnatin ta yi nasarar kaddamar da rabon kayan abinci da suka hada da Shinkafa da Masara a sassan jihar 484. Ya kuma bayyana cewa gwamnati ta kuma kaddamar da rabon kayayyakin koyo da koyarwa, Uniform da jakunkuna/Takalmi, baya ga kaddamar da shirin jigilar dalibai karo na 1 da gwamnati ta dauki nauyin bayar da tallafin karatu a kasashen waje a MAKIA. "Bach na biyu na jigilar daliban da za su je Indiya za a ci gaba da jigilar s...