Posts

Showing posts with the label Jirgin kasa

Gwamnatin Najeriya ta rufe tashar jirgin ƙasa a Edo bayan harin 'yan bindiga

Image
  Copyright: O Hukumomi a Najeriya sun sanar da rufe tashar jirgin ƙasa ta Ekehen da ke jihar Edo, sa'o'i kaɗan bayan hari da 'yan bindiga suka kai tare da yin awon gaba da fasinjojin da ba a san adadinsu ba. Rahotonni sun ce lamarin ya faru ne a daidai lokacin da fasinjojin ke shirin hawa jirgin ƙasan zuwa garin Warri da ke jihar Delta Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Edo Chidi Nwabuzor, ya ce kawo yanzu ba su samu labarin rasa rai ba. To sai dai ya tabbatar da cewa wasu fasinjojin sun samu raunukan harbin bindiga daga maharan. Ya ce 'yan bindigar ɗauke da bindigogi sun far wa tashar jirgin ƙasan da maraicen ranar Asabar, inda suka riƙa harbi a sama kafin su kama wasu da yawa daga cikin fasinjojin. Lamarin na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan da 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari kan jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna a arewacin ƙasar tare da yin garkuwa da fasinjoji ma...

Labari da dumiduminsa : 'Yan bindiga sun sake yin garkuwa da fasinjojin Jirgin kasa

Image
Watanni bayan da ‘yan ta’addan suka kai hari tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama a cikin jirgin kasa zuwa Kaduna, wasu ‘yan bindiga sun kuma kai farmaki tashar jirgin kasa tare da kwashe mutane da yawa a Jihar Edo dake kudu maso kudancin Najeriya. Fasinjojin da suka samu raunuka, an ce suna jiran su hau jirgin kasa a wurin da lamarin ya faru, kafin su nufi garin Warri mai arzikin man fetur. Tuni dai hukumar 'yan sanda ta Rahotanni sun tabbatar da faruwar lamarin a cewar tashar talabijin ta TVC. Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta ce ‘yan bindigar da ke dauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai farmaki tashar jirgin da misalin karfe 4 na yammacin ranar Asabar 7 ga watan Janairu, inda suka yi ta harbe-harbe kafin su fito da shirinsu.  A ranar 28 ga Maris, 2022 ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da wasu fasinjoji. 2022 . Har yanzu dai Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya ba...