Dan China Ya Yi Ikirarin Kashe Wa Marigayiya Ummita Miliyan 60
Dan kasar Chinan nan da ke zargi da kisan budurwarsa, Ummulkusum Buhari (Ummita), Frank Geng Quanrong, ya shaida wa kotu cewa ya kashe wa marigayiyar kudin da yawansu ya kai Naira miliyan 60. Yayin zaman Babbar Kotun Jihar Kano Mai lamba 16 a ranar Laraba, Geng, ya yi ikirarin cewa ya kashe mata kudaden ne a tsawon shekaru biyun da suka yi suna soyayya. “Baya ga manyan kudade da na kashe mata, nakan kai ta wuraren cin abinci kamar a otel din Bristol da Central da sauransu. “Haka kuma na saya mata gida na Naira miliyan hudu da mota ta Naira miliyan 10. Haka kuma na ba ta jarin Naira miliyan 18 don fara kasuwanci baya ga takalma da jakunkuna da na zuba mata a shagon da ta bude na kimanin Naira dubu 500 da kuma atamfofi da lesi na kimanin Naira miliyan daya. Haka kuma na saya mata fili a Abuja inda ta fara ginawa,” in ji dan Chinan A cewarsa, ya saya mata gwala-gwalai da kimarsu ta kai Naira miliyan biyar. “Har ila yau, na saya mata wayar hannu kirar iPhone guda biyu da kudind...