Lauyoyin Emefiele Sun Hana Daukar Hotonsa A Kotu
An kwashi ’yan kallo a kotu bayan lauyoyin dakataccen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele sun nemi hana ’yan jarida É—aukar hotonsa a kotu. Hukumar tsaro ta DSS ce ta yi Æ™arar Emefiele ta kuma kai shi gaban Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Abuja a kan wasu sabbin tuhume-tuhume 20 da Gwamnatin Tarayya ke masa. An ga Emefiele yana yin waya a cikin kotun a safiyar Alhamis, inda lauyoyinsa suka yi ta tattare shi domin hana ’yan jarida É—aukar sa hoto. Bayan kai shi kotun ne kuma alkali ya bukaci dage zaman inda ya bukaci hukumar ta sake gurfanar da Emefiele a ranar 23 ga watan Agustan da muke ciki. Kotu ta dage sauraron Æ™arar DSS ne saboda rashin kawo É—aya wanda ake zargin su tare da Emefiele a zaman kotun na safiyar Alhamis. (AMINIYA)