Na Cika Alkawuran Da Na Daukar Wa ’Yan Najeriya – Buhari
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya cika alkawuran da ya dauka na yaki da ’yan ta’addan boko Haram da farfado da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa. A cewar Kakakin Shugaban, Femi Adesina, Buhari ya bayyana hakan ne yayin wanin taron cin abinci da aka shirya domin karrama shi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe. Giwa ta kashe manomi a Uganda ’Yan bindiga sun harbe jami’an tsaro 12 a Kaduna Shugaban dai ya fara ziyarar yinin biyu ne a Jihar ranar Litinin. Sanarwar ta kuma ce Shugaban ya bigi kirjin cewa babu wanda zai zarge shi da tara dukiyar da ba ta halas ba lokacin da yake mulki, inda ya ce ko taku daya ba shi da shi a wajen Najeriya. A wani labarin kuma, Shugaban ya ce babu wata kungiyar ’yan ta’adda da ta isa ta wargaza Najeriya. Shugaban Kasar ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara fadar Sarkin Damaturu, Alhaji Hashumi Ibn Elkanemi II a fadarsa da ke garin Damaturu, ranar Talata. Buhari ya kuma bukaci ’yan Najeriya da su kara kaimi tare...