Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, ya karɓi bakuncin ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji ta Jihar Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, a Fadar Gwamnati da ke Abuja, inda ya gabatar masa da sabon littafinsa mai taken “Economic Diversification and Structural Transformation in Nigeria: Past, Present, Future.”
A yayin ganawar da suka yi ranar Alhamis, 19 ga Nuwamba, 2026, Jibrin Kofa ya ce ya samu damar miƙa wa Shugaban Ƙasar kwafin littafin, wanda ya mayar da hankali kan tarihin tattalin arzikin Najeriya, halin da yake ciki a yanzu da kuma hanyoyin da za a bi domin samar da tattalin arziki mai ɗorewa.
Ya bayyana cewa littafin, wanda Shugaba Tinubu ya rubuta gabatarwarsa, ya yi nazari kan muhimmancin bunƙasa fannoni daban-daban na tattalin arziki, tare da samar da ingantattun manufofi da za su taimaka wajen sauya fasalin tattalin arzikin ƙasar.
A yayin ganawar, ɗan majalisar ya kuma gabatar wa Shugaban Ƙasa da wasu manyan shirye-shirye guda biyu da ke ƙarƙashin Gidauniyar Abdulmumin Jibrin Kofa, waɗanda suka haɗa da Cibiyar Kasa da Kasa ta Aiwatar da Manufofi da Cigaba Mai Ɗorewa (Global Centre for Policy Implementation and Sustainable Development) da kuma Cibiyar Kasa da Kasa ta Bunƙasa Ma'adinai da Albarkatun Ƙasa (Global Centre for Solid Minerals and Natural Resources Development).
A cewarsa, cibiyoyin za su mayar da hankali kan bincike, samar da sahihan bayanai, bayar da shawarwari bisa hujjoji da ƙididdiga, da kuma aiwatar da manufofin da za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya da amfani da albarkatun ƙasar cikin hikima.
Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da bayar da gudunmawa wajen ci gaban ƙasa ta hanyar bincike, sabbin dabaru, kafa cibiyoyi da samar da manufofin da za su inganta tattalin arziki da walwalar al'umma.
Ya kuma bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin samar da Najeriya mai ƙarfi, wadda za ta samu ci gaba mai ɗorewa da dama ga kowane ɗan ƙasa.
Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, PhD, shi ne ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji ta Jihar Kano.