Kotun Sauraron Korafin Zaben 'Yan Majalisa Ta Soke Zaben Dan Majalisar Tarayya A Kano Bisa Amfani Da Takardun Jabu
Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta Jiha ta tabbatar da cewa Idris Dankawu na jam’iyyar NNPP ya yi jabun takardar shaidar kammala karatu na jarrabawar (WAEC) ya gabatar da shi don tsayawa takarar kujerar dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Kumbotso. Jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa Munir Babba Danagudi ya shigar da karar ne yana rokon ga kotu da ta bayyana cewa Dankawu ya yi jabun satifiket dinsa na Sakandare domin samun gurbin shiga makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic Kaduna. A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a I.P Chima ya yi tir da cewa Idris Dankawu na NNPP ya yi jabun satifiket din sa na WAEC don haka ya soke zaben. Kotun ta umarci INEC da ta ajiye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Dankawu tare da bayyana Munir Babba Danagudi a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Kumbotso na tarayya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Maris. “Da yake mun gamsu da samar da dokar, mun bayyana tare da mayar da Munir Babba Danagudi a matsayin ...