Posts

Showing posts with the label Shari'ar Zaben Gwamnan Kano

Hukuncin Kotu: Sakon Dr Nasiru Yusuf Gawuna Ga Al'umar Kano

Image
Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki daya tabbatar da nasararmu a yau a kotun daukaka kara ta zaben gwamna. Ina so in gode wa kotun daukaka kara saboda hukuncin da ta yanke wanda ya tabbatar da nasarar da muka samu a kotun sauraron kararrakin zabe. Tabbatar da gaskiyar da kotun daukaka kara ta yi tabbas zai karfafa dimokradiyya. Ina so in yi amfani da damar in yaba wa alkalan kotunan zabe da na kotun daukaka kara da suka tsaya kan gaskiya don ganin an yi adalci. Dukkan hukunce-hukuncen biyu sun sake tabbatar da cewa bangaren shari'a shine fata na karshe na talaka. Wannan nasara ce ga daukacin al’ummar jihar nan da mazauna jihar, don haka ina neman goyon bayan kowa ba tare da la’akari da jam’iyya ba don mu hada kai da ni da abokina Alh.Murtala Sule Garo don ci gaban Kano. Dole ne in gode wa jagoranmu mai kaunarmu, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Dr.Abdullahi Umar Ganduje, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sen. Barau Jibrin da Ministoci biyu daga Jihar Kano bisa