Posts

Showing posts with the label Mamu

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Gurfanar Da Tukur Mamu

Image
Wata Babbar Kotu a Jihar Kaduna, ta bayar da umarnin gurfanar mawallafin Jaridar Desert Herald, Alhaji Tukur Mamu a gaban kuliya. Kotu ta nemi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya reshen Jihar Kaduna (SSS) da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami da su gaggauta gurfanar da Mamun ne tare da wasu mutum biyar. Everton ta kori Frank Lampard An tsaurara matakan tsaro a Legas gabanin ziyarar Buhari Bayanai sun ce ababen zargin da kotun ta nemi a gurfanar da su bisa ga madogara ta binciken da aka yi a kansu sun hada; Tukur Mamu, Faisal Tukur Mamu, Ibrahim Hussain Tinja, Abdullahi Mashi, Mubarak Hussain Tinja da Yahaya Bello. Da yake zartas da hukunci kan karar mai dauke da kwanan watan 15 ga Disambar 2022, Alkakin Kotun Mai Shari’a E. Andow, ya ce Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya yi tanadin bai wa duk wani wanda ake zargi ’yancin gurfanar da shi a gaban kuliya hadi da tuhume-tuhume da masu kara za su gabatar. Umarnin kotun na zuwa ne watanni bayan da jami’an tsaron kasa da