Posts

Showing posts with the label Doka

Majalisar Dokokin Kano Za Ta Yi Wa Dokar Masarautu Fyara

Image
A shekarar 2019 dai aka yi wa dokar masarautu a jihar gyara inda aka ƙirƙiro ƙarin masarautu gudu huɗu masu daraja ta ɗaya a jihar. Majalisar ta amince da hakan ne a zaman da ta yi na ranar Talata. Majalisar Dokokin Kano  ta amince a dawo da dokar masarautu ta jihar domin yi mata kwaskwarima. Majalisar ta amince da hakan ne a zaman da ta yi a ranar Talata. A shekarar 2019 gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa dokar masarautu ta jihar gyara inda aka ƙirƙiro ƙarin masarautu gudu huɗu masu daraja ta ɗaya. Masarautun sun haɗa da Gaya da Ƙaraye da Rano waɗanda aka ɗaga darajarsu zuwa masu daraja da ta ɗaya daidai da masarautar Kano. Sai kuma Masarautar Bichi da aka ƙirƙiro, abin da ya sa Kano ta zama tana da masarautu biyar masu daraja ta ɗaya. Masu  adawa da matakin a lokacin sun soki ƙirƙiro sababbin masarautu a Kano domin a cewarsu hakan zai rusa tarihin masaratuar Kano na daruruwan shekaru, inda masarautar take da ƙima a idon duniya saboda faɗinta da kuma tasirinta. Amma

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tantance Lafiya Kafin Aure A Kano

Image
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da dokar tantance lafiyar mata kafin aure a jihar Kano a hukumance, wadda ta tanadi duba lafiyar duk masu son aure. Kamar yadda sabuwar dokar ta tanada, ba za a yi aure ba a Kano ba tare da ba da takardar shaidar tantance lafiyar jinsin halitta, hepatitis B da C, HIV/AIDS, da sauran cututtuka masu alaka da su ba. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce dokar tana ganin ya zama dole domin rage yiwuwar haihuwar yara masu fama da matsalolin lafiya kamar su sickle cell anemia, HIV/AIDS, da hepatitis. Wannan shiri dai ya yi daidai da kudurin gwamnan jihar Kano na inganta da samar da yanayi mai kyau ga fannin kiwon lafiya, da nufin ganin Kano ta kubuta daga matsalolin kiwon lafiya ko kuma rage radadi. Dokar ta wajabta yin gwajin tilas na HIV/AIDS, Hepatitis, genotype, da sauran abubuwan da suka dace kafin aure. Har ila yau, ya haramta duk wani wariya ko kyama ga mutanen

Hukumar PHIMA Ta Rufe Wani Asibiti Bisa Karya Doka

Image
A ci gaba da kokarin da take yi na tsaftace ayyukan cibiyoyin lafiya masu zaman kansu a fadin jihar, hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu ta jihar Kano (PHIMA) ta rufe cibiyar Sassauka Clinic and Diagnosis Centre, Rimin Kebe. Da yake bayar da dalilan da suka sanya aka rufe asibitin, Shugaban hukumar ta PHIMA, Farfesa Salisu Ahmad Ibrahim, ya bayyana cewa hakan ya faru ne sakamakon saba dokokin hukumar da asibitin ke yi. A sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na ma'aikatar lafiya ta Kano, Ibrahim Abdullahi ya sanyawa hannu, yace Farfesa Salisu ya bayyana cewa tun farko sunan asibitin da aka yiwa rajista da PHIMA ya sha bamban da sunan da ake amfani da shi a halin yanzu, inda ya ce sunan asibitin da aka yi wa rajista shi ne Sassauka Clinic and Diagnosis amma yana amfani da asibitin Sassauka ba tare da takardun da suka dace ba wanda zai basu damar yin amfani da shi. canza suna. Shugaban ya ci gaba da bayanin cewa sun kuma kara ayyukansu ba tare da

Dalilin Da Dokar Hana Lefe Ba Za Ta Yi Aiki Ba A Kano

Image
Shi kansa mai laifi ne, domin ya yi lefe a nasa auren da na ’yan uwansa.   Masani a bangaren Shari’a Barista Isa Umar Sulaiman, ya bayyana cewa duk da cewa akwai Dokar Hana Lefe a Kundin Dokokin Jihar Kano, hakan ba zai sa ta yi aiki ba saboda tana kunshe da wasu sharuɗa. Barista Sulaiman ya faɗi haka ne yayin da yake mayar da martani ga fitaccen lauyan nan da ya yi shuhura a kafafen sada zumunta, Barista Abba Hikima. A cewar Barista Sulaiman, neman tayar da kura ko kawo hargitsi ya sanya Barista Hikima ya dago da batun dokar hana lefe a jihar ta Kano. A makon da muke ciki ne dai cikin wani shiri na gidan rediyo a Jihar Kano da kuma shafinsa na Facebook, Abba Hikiman ya dauko batun cewa a Dokar Kano laifi ne ka yi lefe kamar yadda ake yi a yanzu. Wannan magana dai ta ta da kura musamman a soshiyal midiya, inda wasu ke ganin bakinsa wasu kuma ke sam barka. Sai dai Lauya Sulaiman ya ce Hikima tsakuro sashi na 5 na dokar ya yi, ba wai gaba ɗaya dokar kacokan ya fassara ba. “Saɗarar da ya

Barrister Muhuyi Ya Ziyarci Kwamishinan Shari'a, Inda Ya Nemi Yin Gyara A Dokokin Da Suka Kafa Hukumar Da Yake Jagoranta

Image
Shugaban Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimingado ya kai ziyarar aiki ga Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Haruna Isa Dederi, a wani gagarumin ci gaba da aka gudanar da nufin karfafa yaki da cin hanci da rashawa. A cewar wata sanarwa da jami’in yada labarai na ma’aikatar shari’a ta jihar Kano, Musbahu Aminu Yakasai ya fitar, a yayin ziyarar a ranar Alhamis, Rimingado ya tattauna da kwamishinan domin neman goyon bayan gyara dokar hukumar. An tsara gyare-gyaren da ake shirin yi don inganta ingantaccen aiki da ingancin hukumar wajen magance cin hanci da rashawa, inganta gaskiya da kuma tabbatar da bin doka da oda a cikin jihar. Da yake yaba da muhimmiyar rawar da tsare-tsare na shari’a ke takawa wajen yaki da cin hanci da rashawa, Muhuyi Magaji ya nuna jin dadinsa da samun damar hada kai da ma’aikatar. Ya tabbatar da kudurinsa na samar da ingantaccen yanayi na shari’a wanda ke baiwa hukumar yaki da cin hanci