Yan sanda a jihar Kano sun kame 'yan daban siyasa fiye da 60
‘Yan sanda a jihar Kano sun sanar da kame ‘yan daban siyasa akalla 61 yayin wani sumame da suka kaddamar a kokarin kakkabe barazanar rashin tsaro da aikata laifukan da ke ci gaba da tsananta a sassan jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mr Mamman Dauda da ke bayyana hakan a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna ya rabawa manema labarai, ya ce matakin kame ‘yan daban umarni ne daga babban sufeton ‘yan sandan kasar Usman Alkali-Baba.
A cewar sanarwar galibin kamen an yi shi ne yayin gangamin siyasar da ke ci gaba da gudana a sassan jihar, a wani yunkuri na dakile barazanar ‘yan daban dai dai lokacin da babban zaben Najeriya ke ci gaba da karatowa.
A Sanarwar da gidan Rediyon Faransa (RFI) ya wallafa a shafinsa, ta bayyana cewa ta hanyar tsaftace gari daga barazanar ‘yan daban siyasa ne kadai za a iya samun damar tafiyar da harkokin zaben da ke tunakarowa a wata mai zuwa.
Rundunar ‘yan sandan ta jihar Kano ta ce ta gudanar da sumame ranar 4 ga watan da muke na Janairu yayin wani gangamin siyasa da ya gudana a filin wasa na Sani Abacha da ke jihar.
Sanarwar ‘yan sandan ta ce ta kame tarin makamai daga hannun ‘yan daban da suka kunshi wukake 33 da adda guda 8 da almakashi 4 baya ga kunshin tabar wiwi 117.