Gwamna Yusuf Ya Bada Umarnin Biyan Kudaden Always Na Masu Sharar Titina
Da yake nuna damuwa kan cece-kuce da ake yi da kuma ikirari na kin biyan kudaden alawus-alawus na masu shara, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin biyan ma’aikatan cikin gaggawa. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a Kano. Daga nan sai Gwamna Yusuf ya umarci ma’aikatar muhalli da kula da tsaftar muhalli (REMASAB) da ta tabbatar da biyan duk wasu kudaden alawus-alawus na masu shara da suka gada daga gwamnatin da ta gabata. Baya ga haka, Gwamnan ya karyata jita-jitar da ke tada kayar baya na shirin gwamnati na korar masu sharar tituna da suka gada daga gwamnatin da ta gabata, inda ya kara da cewa ba shi da niyyar hana ma’aikatan da ba su yi aiki ba su samu abin dogaro da kai. Alhaji Yusuf wanda ya bayar da wannan umarni a ranar Lahadin da ta gabata yayin wata ganawa da wakilan masu shara a gidan gwamnati, ya nuna rashin gamsuwa da dalilin da ya sa ake jinkirin biya...