Search This Blog

Showing posts with label PDP. Show all posts
Showing posts with label PDP. Show all posts

Sunday, 28 July 2024

Hadakar Jam'iyyun Siyasa A Kano Sun Kauracewa Zanga-zangar Matsin Rayuwa Da Ake Shirin Yi

Jam’iyyar NNPP mau mulki da na adawa da suka haɗa da APC da PDP a unguwar Dakata, Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jihar Kano sun haɗa kai wajen kauracewa zanga-zangar da ake shirin yi kan matsin rayuwa a fadin kasar nan.

Jam’iyyun, ta bakin ciyamonin su na ƙaramar hukumar, sun yi kira ga al’umma da su kauracewa shiga zanga-zangar.

A wani taron gangami da aka yi a Dakata Gidan Dagaci a jiya Asabar, Sabo Sambo (NNPP) da Umar Usman Usman (APC) da na PDP sun gargadi matasa akan illar da zanga-zangar ka iya haifar wa.

A cewar su, akwai sauran hanyoyi da kundin tsarin mulkin ƙasa ya bayar domin neman hajji da yanci daga gwamnati sama da zanga-zanga.

Sun nuna cewa gwamnatin jihar Kano da ta taraiya gana daya shekarar su daya akan mulki, inda su ka kira al’umma da su yi musu uzuri.

“Musamman ma idan aka yi duba na tsanaki za a ga cewa gwamnatin Tinubu da ta jihar Kano, a shekara ɗaya da su ka yi a mulki, sun yi abubuwan yaba wa.

“Za ku ga cewa a bangaren aiyukan lafiya da ilimi da noma duka gwamnatocin sun yi abun yaba wa.

“Saboda haka muna kira gare ku da ku gujewa shiga wannan zanga-zanga wacce ka iya haifar da wata matsalar daban,” in ji su.

Daily Nigeria Hausa

Monday, 11 December 2023

Labari Da Dumiduminsa: 'Yan Majlisar Jahar Rivers 27 Masu Biyayya Ga Wike Sun Bar PDP Zuwa Jam'iyyar APC

Akalla ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas 27 cikin 32 ne suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, sakamakon rikicin da ya barke tsakanin gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ministan babban birnin tarayya (FCT). Nyesom Wike ya zurfafa.


Wani dan majalisar, Enemi George, ya tabbatar wa gidan talabijin na Channels cewa ‘yan majalisar 27 na karkashin jagorancin Martin Amaewhule ne.

'Yan majalisar sun yanke Wannan hukuncin ne a yayin zamansu na safiyar ranar Litinin

(DailyNews24)

Tuesday, 31 October 2023

Kotu Ta Kwace Kujerar Sanatan APC A Kogi, Ta Ba Natasha Ta PDP

Kotun Daukaka Kara ta Ayyana Natasha Akpoti ta jam’iyyar PDP a matsayin halastacciyar wacce ta lashe zaben kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai a watan na Fabrairu ta ayyana Sanata Abubakar Ohere na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, amma Natasha ta garzaya kotu.

Daga bisani dai kotun sauraron kararrakin zabe da ke Jihar Kogi ta soke zaben na Ohere, sannan ta tabbatar mata da nasara.

Kotun dai, wacce Mai Shari’a K.A Orjiakor ya jagoranta, ta ce an yi wa Ohere aringizon kuri’u a wasu rumfunan zabe tara da ke Karamar Hukumar Ajaokuta.


Alkalin ya ce an kuma cire sakamakon Natasha a mazabun da karin wasu guda uku, duka dai a cikin Karamar Hukumar.

Hakan ne ya sa kotun ta ayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaben da kuri’u sama da 54,074, sabanin kuri’a 51,291 da ta ce Ohere ya samu.


Sai dai Sanatan bai gamsu da hukuncin ba, inda daga bisani ya garzaya kotun daukaka karar, amma ta tabbatar da hukuncin kotun bayan.

(AMINIYA)

Monday, 16 October 2023

Jami'an Tsaro Sun Rufe Ofishin PDP Na Jahar Ondo

Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS da kuma ’yan sanda sun rufe sakatariyar jam’iyyar adawa ta PDP ta Jihar Ondo.

Hukumomin tsaron sun dauki matakin ne a safiyar Litinin a daidai lokacin da al’ummar jihar suke gunaguni da neman gwamnatin jihar ta bayyana musu inda Gwamna Rotimi Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki.

Yadda Ba Da Dala Ga Masu Shigo Da Shinkafa Zai Shafi Farashin Ta Gida
Ganduje ya lashi takobin kare kujerar gwamnan Nasarawa da kotu ta kwace
Ana zargin hukumomin tsaron sun rufe ofisihin jam’iyyar ne sakamakon shirin wasu ’yan jam’iyyar na gudanar da zanga-zanga kan rashin kasancewar gwamnan a jihar na tsawon lokaci.

Da farko Gwamna Akerodule wande ke fama da rashin lafiya da ba a bayyana ba, ya shafe wata uku a kasar Jamus, inda yake jinya, kafin ya dawo jihar a watan Satumba.


Tun bayan dawowar gwamnan, ya ci gaba da zama a gidansa, da ke birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, lamarin da ya sa babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar kiraye-kirayen ya sauka daga mukaminsa.

A ranar Lahadi PDP ta yi barazanar jagorantar wani gagarumin zanga-zanga a birnin Akure a yau Litinin, domin neman sanin inda Mista Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki da ya hana shi zama a Jihar Ondo.


Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani kan halin da ake ciki daga kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo Funmilayo Odunlami-Omisanya, amma hakar ba ta cim-ma ruwa ba.
(AMINIYA)


Friday, 28 April 2023

PDP Ta Bukaci Sanyawa Buhari Takunkumi

Babbar jam’iyyar adawar Najeriya ta PDP ta bukaci kasashen duniya da su hana shugaban kasa Muhammadu Buhari bizar tafiye tafiye da zaran ya mika mulki ranar 29 ga watan gobe, saboda abinda ta kira kalamansa dangane da zaben shugaban kasar da akayi ranar 25 ga watan Fabarairu. 


Yayin tsokaci akan zaben, Buhari ya bayyana ‘yan adawar Najeriya a matsayin wadanda suka shantake akan cewar zasu samu nasara ba tare da neman goyan bayan jama’a kamar yadda jam’iyarsa ta APC tayi ba. 

Sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar Debo Ologunagba yace kalaman shugaban na iya tinzira jama’a da kuma haifar da illa ga zaman lafiyar kasar. 

Ologunagba ya kuma ce kalaman na iya karfafawa alkalai gwuiwa wajen yanke hukunci akan karar da suka shigar a gaban kotu domin kalubalantar sakamakon zaben wanda yace tuni wasu a ciki da wajen kasar ke bayyana shi a matsayin mafi muni a tarihin Najeriya. 

Jam’iyyar PDP tace zaben da akayi bana ya gamu da matsalolin da suka sabawa kundin tsarin mulkin kasa da kuma dokar zabe ta shekarar 1999 da kuma 2022 musamman abinda ya shafi wallafa sakamako daga tashoshin zabe da kuma aikewa da su kai tsaye zuwa cibiyar hukumar ta kasa. 

Kakakin jam’iyyar ya jaddada cewar suna da yakinin cewar basu fadi zabe ba, kamar yadda shugaba Buhari ke fadi, kuma ba zasu bada kai bori ya hau ba duk da barazanar da gwamnatin APC ke musu. 

Jam’iyyar tace ganin yadda Buhari ya yiwa dimokiradiya illa a Najeriya, suna bukatar kasashen duniya da su kakaba masa takunkumi da kuma hana shi da iyalansa tafiye tafiye da zaran ya mika mulki ranar 29 ga wata. 

Ologunagba yace wannan bukatar tasu tayi dai dai da bukatar da shugaba Buhari ya gabatarwa kungiyar kasashen Turai a ranar 17 ga watan Fabarairun shekarar 2022 lokacin da ya ziyarci kungiyar EU a Brussels. 

RFI

Friday, 31 March 2023

Gobara Ta Barke A Gidan PDP

 


Ga dukkan alamu gobara ta sake barkewa a gidan babbar jam’iyyar adawa ta kasar nan wato PDP, wadda ta sake shiga rudu, makonni kadan da faduwarta a zaben Shugaban Kasa.

A ranar Talata da ta gabata ce, Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na Kasa (NWC), ya ayyana Ambasada Iliya Umar Damagum a matsayin Shugaban Riko na jam’iyar ta kasa.

Kafin nadinsa, Alhaji Iliya Damagum shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Shiyyar Arewa.

Kakakin Jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba ne ya bayyana nada Damagun a ranar Talata a wani taron manema labarai a Abuja.

A sanarwar da PDP ta fitar, ta ce ya zame mata dole ta yi biyayya ga umarnin wata kotu da ta bukaci Shugaban Jam’iyyar na Kasa Dokta Ayu Iyorchia ya daina bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan kararsa da aka kai gabanta.

Wata Babbar Kotu a Jihar Benuwai ce ta dakatar da Dokta Iyorchia Ayu daga shugabancin Jam’iyyar PDP ta Kasa.

Alkalin Kotun, Mai Shari’a W.I Kpochi ne ya bayar da umarnin a ranar Litinin bayan sauraron kunshin karar da aka shigar Mai lamba MHC/85/2023.

Tun a ranar Juma’ar da gabata Jam’iyyar PDP ta ce ta dakatar da Shugabanta na Kasa, Iyorchia Ayu bisa zarginsa da wasu ayyuka na cin amanar jam’iyyar.


Shugabannin jam’iyyar a matakin gundumarsa da ke Karamar Hukumar Gboko, a Jihar Benuwe ne suka dauki matakin.

Sun ce sun dakatar da shi ne bayan kada kuri’ar rashin kwarin gwiwa kan ayyukansa.

A lokacin da ya karanta matsayar da shugabannin suka cim ma, Sakataren Jam’iyyar a Gundumar Igyorob, Mista Banger Dooyum ya ce zagonkasa da Ayu da na kusa da shi suka yi wa PDP ne ya janyo mata shan kaye a gundumar da kuma jihar baki daya a zaben Gwamnan da aka yi a jihar.

Sun kuma zargi Ayu da rashin biyan kudaden da ake karba na shekara-shekara daga ’ya’yan jam’iyyar, kamar yadda dokokinta suka tanada.

hugaban Kungiyar, Terzungwe Atser ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar, inda a ciki ya ce ba zai taba yiwuwa jagororin jam’iyyar su dauki wannan mataki ba a yanzu ba tare da an tursasa su yin hakan ba.

Yanzu aka fara rigimar —Wike

A bangaren Gwamnan Jihar Ribas, Nyesome Wike ya ce yanzu aka fara rigimar siyasa a tsakaninsa da dakataccen shugaban na PDP, Dokta Ayu.

Ya ce hankali ba zai dauka ba a ce wanda ya kasa kawo mazabarsa a zabubbukan da suka gabata ya ci gaba da jagorantar PDP a matsayin Shugabanta na kasa.

Wike ya bayyana haka ne lokacin da yake kaddamar da makarantar Okoro-nu-Odo da ke Karamar Hukumar ObioAkpor da ya sabunta.

Ya ce, Allah ne kadai Ya san dalilin da Ayu ya kekeshe zuciyarsa ya ki sauka daga mukaminsa a lokacin da Gwamnoni 5 da ake kira G5 suka bukaci hakan bayan Atiku Abubakar ya zama dan takarar Shugaban Kasa a PDP.

Gwamna Wike ya ce da a ce lokacin da suka bukaci haka, Dokta Ayu ya amince ya sauka, da irin su da suka yi kokarin ganin an mayar da mulki Kudu sun yi amfani da wannan wajen samun sulhu, wanda a cewarsa watakila da hakan ya sa Jam’iyyar PDP ta samu nasara.

“Ku wadanda kuke cewa kun dakatar da Ayu, ba ku ma ga komai ba.

“Ayu, yanzu aka fara rigimar nan. Wadanda suke kusa da shi su fada masa cewa yanzu aka fara,” in ji Wike.

Duk da cewa ba yanzu aka fara yunkurin cire Ayu daga Shugaban PDP na Kasa ba, wannan karon lamarin ya yi karfi matuka domin a cikin shugabannin jam’iyyar da masu ruwa-da-tsaki an samu rabuwar kai kan cire shi.

Aminiya ta samu labarin cewa an fara yunkurin ganin bayansa ne kwanaki kadan bayan zaben Shugaban Kasa, inda Jam’iyyar PDP ta sha kaye a hannun Jam’iyyar APC, rashin nasarar da wasu suka alakanta da kin amincewa ya sauka daga mukaminsa.

Aminiya ta ruwaito yadda hayaki ya fara tashi a jam’iyyar bayan Atiku Abubakar ya doke Gwamna Wike na Ribas a zaben fid-da-gwan na takarar Shugaban Kasa.

Gwamna Wike da wasu gwamnoni hudu sun ware, inda suka kafa Kungiyar G5, wadda daga cikin bukatunta akwai batun cire Ayu a matsayin shugaban jam’iyyar.

A cewarsu, ba zai yiwu ba dan takarar Shugaban Kasa da Shugaban Jam’iyya su fito daga yanki daya, wanda hakan ya sa suka bukaci Ayu ya sauka, a musanya shi da wani daga Kudu.

Hakan ya sa PDP ta shiga zaben Shugaban Kasa ba tare da gwamnonin biyar tare da ita ba, ciki har da Wikem, Gwamnan Jihar Ribas wadda take kan gaba wajen ba PDP kuri’u a zabubbukan baya.

Aminiya ta samu labarin cewa wannan yunkurin ya kara zafi ne kasancewar shugaban ya kasa hada kan jam’iyyar kafin zabe da kuma gazawarsa wajen kawo wa PDP jiharsa a zaben Shugaban Kasa da na gwamnoni, duk da cewa ba sa ga maciji da Gwamnan jiharsa ta Binuwai daya daga cikin gwamnonin G5.

Wasu abubuwan da suka kara ta’azzara rikicin shi ne batun dakatar da wasu jiga-jigan Jam’iyyar PDP da suka hada da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema kuma ta bukaci Kwamitin Ladabtarwa na Jam’iyyar da ya binciki Gwamna Ortom na Binuwai.

Jim kadan bayan dakatar da Shema ne ya fitar da sanarwa, inda a ciki ya bukaci ko dai a janye dakatarwa, ko ta zama takardar sallamarsa daga jam’iyyar, domin a cewarsa ba zai yiwu a dakatar da shi ba, inda kuma aka ce dole za a dakatar da shi, to zai bar jam’iyyar.

Daga cikin wadanda suke gaba-gaba wajen ganin an cire Ayu, akwai gwamnonin G5, wato Gwamna Nyesom Wike na Ribas da Samuel Ortom na Binuwei da Seyi Makinde na Oyo da Okezie Ikpeazu na Abiya da Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Akwai kuma wasu jigajigan jam’iyyar, ciki har da tsofaffin gwamnoni da suka hada da Ibrahim Shema da Cif Bode George da Ayo Fayose da sauransu.

Haka a cikin jagororin jam’iyyar, Aminiya ta samu labarin cewa an samu rarrabuwar kai a tsakaninsu, inda wasu suka amince a cire shi, wasu kuma suke tare da shi.

Akwai bayanan da suke cewa mai yiwuwa Dokta Ayu ya kalubalanci dakatar da shi da Kwamitin NWC ya yi a kotu, lamarin da ake jin zai kara rura wutar rikicin da ke cin jam’iyyar.

AMINIYA

Friday, 10 February 2023

Labari da dumiduminsa : Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Sadiq Wali A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Kano Na PDP

A ranar Juma’a ne wata kotun daukaka kara ta jihar Kano ta tabbatar da Sadiq Aminu Wali a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Kano.


A wani hukunci na bai daya da ta yanke a ranar Juma’a, kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da karamar kotun ta yanke na tabbatar da Muhammad Abacha a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano na PDP.

Cikakkun labarin zai zo muku nan ba da jimawa ba…

Thursday, 2 February 2023

Kotun Koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari a matsayin 'Yar Takarar Sanatan PDP Ta Kano Tsakiya

A ranar Alhamis ne kotun koli ta sake tabbatar da Hajiya Laila Buhari a matsayin ‘yar takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar PDP.

SOLACEBASE ta ruwaito cewa a baya kotun daukaka kara ta tabbatar da Laila Buhari ta soke zaben Danburan Nuhu.

Kotun kolin da ta yanke hukuncin da mai shari’a Muhammad Lawal Garba ya karanta, ta yi watsi da dukkan dalilan daukaka kara ta Danburam Nuhu.

Jastis Garba na tare da Jastis Kudirat Kekere Ekun, da Jastis Saulawa da Jastis Ibrahim Jauro, da Jastis Emmanuel Agim

Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Friday, 27 January 2023

2023PDP Ce Ta Haifar Da Wahalar Man Fetur A Najeriya – Tinubu


Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya ce dillalan man da PDP ta bai wa lasisi zamanin mulkinta ne ke boye fetur yanzu a Najeriya.

Tinubu ya kuma ce magoya bayan PDPn da jam’iyyar ta bai wa lasisin zamanin mulkinta ne ke yin hakan saboda dalilan siyasa da kuma haddasa dogayen layuka a gidajen mai.

Idan muka je saro kaya da tsoffin kudi ba a karba – ’Yan kasuwar Gombe
‘Duk Shugaban Kasar da zai zo zai fuskanci kalubale irin na Jonathan da Buhari’
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin gangamin yakin neman zabensa da ya gudanar a Jihar Binuwai ranar Alhamis.

Ya ce, PDP Jam’iyya ce ta ruruta wutar talauci ce, musamman idan aka yi la’akari da yadda ’yan Najeriya ke shan bakar wahala a yanzu.


Sun bai wa magoya bayansu lasisin da yanzu ya haifar da dogayen layuka na jabu a gidajen mai. PDP haka ya ishe ku fa!”

Ya kuma ce rashin sanin doka ne ya sanya abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar, ya ce kasuwancin sufuri yake a lokacin da yake aiki da Hukumar Hana Fasakwauri ta Kasa, lokacin da yake amsa tambayar da wasu suka yi masa kan yadda ya yi arziki haka.

“Suka tambaye shi ya aka yi ya yi arziki da yake da shi, sai ya kada baki ya ce kasuwancin sufuri yake. Bai san cewa laifi ne babba ba a ce kana ma’aikacin gwamnati kuma ka yi wani aikin ba noma ba,” in ji Tinubu.
Tsohon Gwamnan Jihar Legas din ya kuma ce yana da yakinin yadda ya ciyar da jiharsa gaba lokacin da ya jagoranceta, zai tabbatar ya yi wa Najeriya haka.
AMINIYA 


Wednesday, 18 January 2023

Duk Mai Son Mukami A Gwamnanatina Sai Ya Kawo Akwatinsa Lokacin Zabe - Atiku

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce duk dan jam’iyyar da ke neman kwagila ko mukami a gwamnatinsa, sai ya nuna sakamakon zaben mazabarsa kafin a ba shi.

Atiku ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Abekuta babban birnin Jihar Ogun, yayin taron ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.

Atiku ya ce halartar kowanne yakin neman zaben jam’iyyar ba shi ne tabbacin samun matsayi ko kwangila a gwamnatinsa ba, jajircewa wajen ganin an kawo akwatinan mazaba ne.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma ce, “Dukkanku magoya bayan PDP ne, kuma kuna so ta dawo mulki, don haka ina rokonku ku tabbatar kun kawo akwatinan mazabunku.

Yawon zuwa yakin neman zaben kafatanin ’yan takarar jam’iyya ba shi ne zai sa ka samu aiki ko matsayi ko kwangila ba idan an ci zabe, hanyar da kadai za ku samu shi ne nuna min sakamakon zaben mazabarku.

“Kuma ina bai wa kowanne dan takarar PDP umarnin yin hakan, domin da haka ne kadai za mu ci zabe.

Atiku ya kuma yi alkawarin farfado da bangaren ilimi da tattalin arziki, domin kawo karshen yajin aikin jami’o’i a Najeriya, da kuma inganta rayuwar ma’aikata da sauran al’umma.
(AMINIYA) 

Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

FG Urges KOICA, FAO to Align Agricultural Intervention with Nigeria’s Development Priorities, Ward-Based Strategy

The Federal Government has called for stronger alignment between development partners’ interventions and Nigeria’s national deve...