Ta’addanci: Ba Don Taimakon Majalisar Dinkin Duniya Ba Da Mun Banu — Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara ɓullo da ƙwararan matakan tallafa wa Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci. Tinubu ya mika wannan kokon bara ne kan abin da ya kira mummunar illar ta’addanci ga zaman lafiyar duniya da yadda yake tarwatsa mutane da ƙara haifar da fatara. ECOWAS ta musanta neman sojojin Nijar su mika wa farar-hula mulki nan da wata tara Yadda UEFA ta fitar da jadawalin Gasar Zakarun Turai ta bana Ya yi wannan kira ne lokacin da yake jawabi yayin ganawa da ƙaramin sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya kan yaƙi da ta’addanci, Mista Vladimir Voronkov, a fadar gwamnati. Shugaba Tinubu ya nunar da cewa ta’addanci ya yi ta mayar da hannun agogo baya ga harkokin ci gaban ƙasa da janyo ƙarin rashin kwanciyar hankali a tsakanin iyalai da al’ummomi Ya bayyana ce ayyukan haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya wajen tunkarar matsalar, sun kasance a tsittsinke kuma ana samun katsewar irin wannan tallafi ga ƙasashe masu tasowa. “Ya zama tilas daf