NAHCON Ta Gana Da Mai Kamfanin Da Ke Yi Wa Alhazan Najeriya Hidima, Inda Ta Nemi Sake Inganta Ayyukansa
Mukaddashin Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), Malam Jalal Ahmed Arabi OON, fwc, ya yi kira ga Hukumar Alhazai ta Saudi Arabiya, Mutawiff na kasashen da ba na Larabawa ba, da su kara habaka hidima ga mahajjatan Nijeriya a kasar. a lokacin zaman Masha'ir. A yayin wata ganawa a ofishin Hukumar da ke Abuja tare da Dakta Ahmad Abbas Sindi, Shugaban Hukumar, ya jaddada muhimmancin hada kai don nemo hanyoyin magance matsalolin da aka fuskanta a lokacin aikin Hajjin 2023. A sanarwar da Mataimakin daraktan yada labarai na hukumar, Mousa Ubandawaki ya sanyawa hannu, yace Taron wanda ya samu halartar wasu sakatarorin hukumar jin dadin alhazai ta jiha, shuwagabanni da mambobin kungiyar masu gudanar da aikin Hajji da Umrah ta Najeriya (AHUON), ya tattauna matsalolin da suka shafi hidimar zaman Mina da Arfah a lokacin aikin Hajjin 2023 tare da bayyana shirye-shiryen aikin Hajjin 2024. , musamman a fannonin ciyarwa, sufuri, rabon tantina, tsaro, da maida kuÉ—i, da dai saur