Posts

Showing posts with the label Majalisar Dattijai

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Sale, Zai Fara Aiki A Matsayin Shugaban Riko Kafin Majalisar Dattijai Ta Tabbatar Da Nadinsa

Image
Farfesa Abdullahi Sale Usman wanda aka nada a matsayin shugaban hukumar alhazai ta kasa NAHCON, zai fara gudanar da aikinsa a matsayin Shugaban riko har sai majalisar dattawa ta amince da nadin.  Wannan tsari dai zai kasance har sai majalisar dattawa ta dawo daga hutu domin tattaunawa kan nadin nasa. Hakan na kunshe ne a wata takarda da jaridar Hajj Chronicles ta gani, mai kwanan wata 5 ga Satumba 2024, kuma mataimakin shugaban ma’aikata a ofishin mataimakin shugaban kasa, Ibrahim Hassan Hadejia ya sanya wa hannu.  Wasikar ta bayyana cewa Farfesa Usman zai sa ido kan ayyukan Hukumar yayin da yake jiran amincewar majalisar dattawa. Nadin Farfesa Usman ya samu gagarumin goyon baya saboda dimbin gogewa da gudummawar da ya bayar a fannin aikin Hajji a Najeriya, musamman a jahar Kano lokacin da ya rike matsayin shugaban Hukumar Alhazai ta Kano  Ana sa ran tabbatar da shi a zaman majalisar da zarar ta koma hutu

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Ya Yi Alkawarin Taimakawa Wajen Bunkasa Ilimi

Image
  Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya tabbatar wa shugabannin Jami’ar Bayero Kano (BUK) goyon bayan da suke ci gaba da ba su wajen magance kalubalen da ke addabar cibiyar da bangaren ilimi a jihar da ma kasa baki daya. A sanarwar da mashawarcinsa na musammam harkokin yada yada labarani,b Ismail Mudashir  ya sanyawa hannu, yace Sanata Barau ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da shugabannin jami’ar karkashin jagorancin mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, suka kai masa ziyarar ban girma a majalisar dokokin kasa, Abuja, a ranar Laraba 1 ga watan Nuwamba, 2023. Mataimakin shugaban majalisar ya yabawa mataimakin shugaban majalisar dattijai bisa goyon bayan da ya bayar tare da neman taimakonsa wajen magance kalubalen da cibiyar ke fuskanta. Musamman, ya yi kira ga Sanata Barau da ya taimaka wajen samar da masauki ga daliban likitanci a yankunan karkara kamar yadda Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) ta t...