Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa an yi artabu tsakanin jami’an SSS da Mista Emefiele kan zargin bada tallafin yaki da ta’addanci.
A baya dai hukumar leken asirin ta nemi kotu ta kama Mista Emefiele amma ya fita kasar domin hutun shekara da zai kare a gobe 17 ga watan Janairu.
Sai dai a watan Disamba ne babbar kotun birnin tarayya ta haramtawa SSS kama, gayyata, ko kuma tsare Mista Emefiele.
Jami’an SSS da suka isa hedikwatar CBN a ranar Litinin da ta gabata, sun shigo da motoci kusan 20 dauke da jami’an tsaro.
Jami’an sun kuma hana duk ma’aikatan bankin shiga ofishin Mista Emefiele.
Peter Afunanya, mai magana da yawun SSS, har yanzu bai amsa tambayar da dan jaridan ya aike masa ba.
Cikakkun bayanai daga baya…