Posts

Showing posts with the label Fasfon

Jinkirin Mika Fasfon Maniyyata Na Kawo Cikas Ga Aikin Yin Bizar Aikin Hajji - Laminu Rabi'u

Image
Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa, ya bayyana  jinkirin mika fasfo  ga hukumar a matsayin  babban kalubalen da ke kawo cikas wajen yin Bizar aikin Hajji ga maniyyata Yayin wata ziyara zuwa daya daga cikin cibiyoyin bitar Alhazai  da aka gudanar a karamar hukumar Doguwa a yau, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ya jaddada muhimmancin bayar da fasfo a kan lokaci wajen saukaka gudanar da bizar aikin Hajji cikin sauki ga maniyyata. A cikin sanarwar da Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Sulaiman Abdullahi Dederi ya sanyawa hannu, yace Alhaji Danbappa, wanda wakilin hukumar gudanarwa na hukumar, Malam Ismail Mangu ya wakilta, ya bayyana cewa, “jinkirin tura fasfo na kasa da kasa yana kawo cikas wajen gudanar da aikin Hajji yadda ya kamata ga maniyyatan mu, ya zama wajibi mu daidaita wannan aiki domin tabbatar da kammala aikin a kan lokaci. da kuma inganta aikin hajji gaba daya”. Malam Ismail Mangu ya kara jaddada muhimmanc