Posts

Showing posts with the label Kotun Daukaka Kara

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Gwamna Abdullahi Sule Na Jahar Nassarawa

Image
Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da zaben gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule.  Kotun daukaka kara ta kuma yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Nasarawa ta yanke a ranar 2 ga watan Oktoba da ta kori Sule na jam’iyyar APC tare da bayyana David Ombugadu, dan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.  Da yake yanke hukunci, kwamitin mutum uku ya ce kotun ta yi kuskure wajen yanke hukuncin cewa Gwamna Sule bai samu rinjayen kuri’un da aka kada a zaben ba.  Cikakken labarin zai zo muku nan gaba 

Labari Da Dumiduminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Kebe Hukuncin Da Za Ta Yi Kan Zaben Gwamnan Kano

Image
Idan dai za a iya tunawa,Dan takarar jam’iyyar  APC Nasiru Yusuf Gawuna, ya lashe zaben.  Kwamitin mutum uku na kotun karkashin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ya kori Yusuf a ranar 20 ga watan Satumba, 2023, bayan ya zare kuri’u 165,663.  Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta sanar da cewa Yusuf ne ya lashe zaben ranar 18 ga Maris, 2023, inda ta ce ya samu kuri’u 1,019,602 inda ya doke Gawuna wanda ya samu kuri’u 890,705. Sai dai jam’iyyar APC ta tunkari Kotun, bisa zargin tafka magudin zabe.  Kotun da ta amince da APC ta soke zaben Yusuf, inda ta kara da cewa sama da katunan zabe 160,000 “ INEC ba ta sanya hannu ko tambari ba. An rage kuri’un Yusuf zuwa 853,939 yayin da kuri’u 890,705 Ganuwa bai shafa ba.  Daga nan sai gwamnan ya shigar da kara a gaban kotun daukaka kara. Jam’iyyun APC da INEC da NNPP su ma sun shigar da kara a gaban kotun. A ranar Litinin, babban lauyan gwamnan, Wole Olanipekun SAN (wanda shi ne babban lauyan Tinubu a PEPC), ya bukaci kotun

Kotu Ta Kwace Kujerar Sanatan APC A Kogi, Ta Ba Natasha Ta PDP

Image
Kotun Daukaka Kara ta Ayyana Natasha Akpoti ta jam’iyyar PDP a matsayin halastacciyar wacce ta lashe zaben kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya. Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) dai a watan na Fabrairu ta ayyana Sanata Abubakar Ohere na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben, amma Natasha ta garzaya kotu. Daga bisani dai kotun sauraron kararrakin zabe da ke Jihar Kogi ta soke zaben na Ohere, sannan ta tabbatar mata da nasara. Kotun dai, wacce Mai Shari’a K.A Orjiakor ya jagoranta, ta ce an yi wa Ohere aringizon kuri’u a wasu rumfunan zabe tara da ke Karamar Hukumar Ajaokuta. Alkalin ya ce an kuma cire sakamakon Natasha a mazabun da karin wasu guda uku, duka dai a cikin Karamar Hukumar. Hakan ne ya sa kotun ta ayyana ta a matsayin wacce ta lashe zaben da kuri’u sama da 54,074, sabanin kuri’a 51,291 da ta ce Ohere ya samu. Sai dai Sanatan bai gamsu da hukuncin ba, inda daga bisani ya garzaya kotun daukaka karar, amma ta tabbatar da hukuncin kotun bayan. (AMINIYA)