Posts

Showing posts with the label Messi

Saudiyya Ta Yi Wa Messi Tayin Ninkin Albashin Ronaldo

Image
  Kungiyoyin kwallon kafa a kasar Saudiyya na zawarcin gwarzon dan wasan duniya, Lionel Messi, na kungiyar PSG, da tayin albashin da ya zarce na kowane dan wasa a duniya. Rahotanni sun nuna cewa wata kungiya da ke zawarcin Messi a Saudiyya ta yi masa tayin albashin Naira biliyan 183.5 (Dala miliyan 400) a shekara, idan kwantaraginsa ya kare da PSG a wata mai zuwa. Kafar labarai ta Telegraph ta kasar Birtaniya ta ce dan wasan ya fara tunanin duba tayin kuma tuni kungiyar ta fara tattaunawa da Kyaftin din na kasar Argentina kan kwangilar da take masa tayi, bayan dakatarwar da PSG ta yi masa. Idan hakan ta tabbata, Messi zai rika karbar kusan ninki biyun albashin babban abokin hamayarsa Cristiano Ronaldo, wanda a halin yanzu Al Nassr ta kasar Saudiyya ke biyan sa Naira biliyan 96.3 Dala miliyan 210 a shekara, zuwa 2025. A halin yanzu dai, Cristiano Ronaldo ne dan wasa mafi albashi a duniya, inda Messi ke biye da shi, kafin Kylian Mbappe na Farasan da PSG. Wannan sabuwar ta taso ne bayan d

Messi da Mbappe da Neymar sun yi wasa tare karon farko bayan kofin duniya

Image
A ranar Lahadi Kylian Mbappe da Lionel Messi da kuma Neymar suka buga wa Paris St Germain wasa tare karon farko tun bayan kammala Gasar Kofin Duniya a Qatar. Argentina ce ta lashe kofin da Messi ya daga, bayan da suka yi nasara a kan Faransa tawagar Mbappe, yayin da Brazil ta Neymar ba ta kai bante ba. Sun kuma buga wasan Ligue 1 na faransa fafatawar zagaye na 19, inda Rennes ta yi nasara da ci 1-0. Tun farko an bai wa Messi karin lokacin hutu, domin ya samu damar murnar lashe kofi da suka yi wa kasar na uku jumulla Sai dai kuma Messi ya ci kwallo da ya koma yiwa PSG tamaula a tsakiyar mako da ta tashi 2-2 da Angers. Shi kuwa Mbappe bai samu buga wasa biyu ba, bayan da ya je hutu birnin New York tare da abokinsa Achraf Hakimi. An sa ran za a fara wasa da Mbappe ranar ta Lahadi, sai ya fara da zaman benci daga baya ya canji Hugo Ekitike, inda ya hadu da Messi da Neymar daga gaba.