Rashawa: Yau Za A Ci Gaba Da Shari’ar Ganduje
Wakilin majiyarmu a kotun ya ruwaito cewa lauyoyin bangarorin sun zauna, ana jiran isowar alkalin kotun. Za a ci gaba da zaman ne bayan gaza gurfanar da Ganduje da sauran wadanda ake zargi a lokacin zaman farko ranar 17 ga wata, a shari’ar da hukumar yaki da almundahana ta jihar Kano ta shari’ar da shigar kara. Hukumar na zargin Ganduje da mai dakinsa da dansa da wasu makusantansa da laifuka takwas da suka danganci rashawa da karkatar da dukiyar al’umma. ِShugaban hukumar, Muhyi Magaji Rimin Gado, ya zargi gwamnatin Ganduje, da karkatar da kudaden kananan hukumomi Naira biliyan 51.3. A cewarsa, hukumar ta bankado yadda tsohuwar gwamnatin ta ciri Naira miliyan 600 daga asusun gwamnatin Kano zuwa wani kamfani da Ganduje yake darakta kuma mai dakinsa ce ke gudanar da asusunsa. Muhuyi ya ce za su gabatar da shaidu da hujjoji 15 kan zargin da ake wa tsohon gwamnan a gaban a gaban Babbar Kotun Jihar Kano. Sai dai rashin bayar da sammaci ga Ganduje da matarsa da dansa da wasu mutane biyar ya