Posts

Showing posts with the label Sata

Jita-Jitar Satar Naira Biliyan 50 a NAHCON: Babu Shaida, Babu Gaskiya - Ganiyu Lamidi

Image
Daga Ganiyu Lamidi A Najeriya, jita-jita kan zama kamar gaskiya idan aka yi ta maimaitawa. Labaran karya kan shafe na gaskiya, saboda mutane suna son jin labaran Al'ajabi, shakku ko mamaki. Mun taba jin labarin Madam Koi-Koi da Iliya dan Mai-Karfi, duk da ba gaskiya ba ne, amma mutane sun dade suna yada wannan labaran. Yanzu haka, Hukumar Alhazan Najeriya, NAHCON, da Shugabanta Farfesa Abdullahi Saleh Usman, sun fada cikin irin wannan jita-jitar. Zargin wai an sace Naira biliyan 50 a hajjin da ya gabata. Labarin ya yadu Kamar wutar daji a kafafen sada zumunta da jaridu, amma babu wata hujja ko gaskiya cikin lamarin. Zargi ne kawai da 'Yan siyasa ke kara rura wutarsa. Idan muka duba lamarin a hankali, za mu ga cewa wannan magana bata da tushe. A 2025, alhazai daga kudanci sun biya kusan Naira miliyan 8.78, yayin da na arewa suka biya Naira miliyan 8.46. Idan aka raba Naira biliyan 50 da wannan farashi, zai bamu adadin alhazai kusan 5,700. Wato sai mutum ya karbi kudi...

Bakuwa Ta Sace Jariri Awa 3 Da Haihuwarsa A Asibiti

Image
  Ana zargin bakuwa ta sace jaririn ne da hadin bakin ’yar uwar mai jegon Wata mata ta sace jariri awa uku bayan haihuwarsa a Asibitin Kwararru na Dalhatu Arafat (DASH) da ke garin Lafia, Jihar Nasarawa. Ana zargin bakuwar ta sace jaririn ne da hadin bakin ’yar uwar mai jegon sa’o’i kadan da haihuwarsa ta hanyar yi wa mahifiyarsa tiyata. Aminiya ta gano bayan haihuwarsa da misalin karfe 3 na asubahin ranar Talata ne jami’an asibiti suka mika jaririn da mai jegon ga wata ’yar uwarta domin ta ci gaba da kula da su. Wani ganau da ya nemi a boye sunasa ya ce, bayan sun dawo dakin masu jego ne ’yar uwar mai jegon ta kawo mata da wata bakuwa, wadda ake zargin sun hada baki wajen sace jaririn. ‘Kamar Layar Zana’ A cewarsa, “’yar uwar mai jegon ce ta ce mata za ta koma gida ta dauko cajar wayarta da ta manta; shi ne ta hada ta da wata mata da za ta zauna da su kafin ta dawo ,” wadda ake zargin ita ce ta sace jaririn. Sace jaririn daga dakin masu jegon da misalin karfe 6 na safe,  awa ...

Dan shugaban kasar Guinea ya sace jirgin sama na gwamnati

Image
An kama daya daga cikin ‘ya’yan shugabaan Equatorial Guinea kan zargin sa da sace tare da sayar da wani jirgin sama mallakin gwamnatin kasar. An tsare Ruslan Obiang Nsue a ranar Litinin, sannan aka yi masa daurin talala kamar yadda kafar talabijin ta kasar ta bayyana. Tun a cikin watan Nuwamban da ya gabata, aka kaddamar da bincike bayan hukumomi sun gano cewa, daya daga cikin jiragen gwamnati mai lamba ATR 72-500 ya yi batan-dabo  a filin jiragen sama na kasa da kasa. A shekarar 2018 ne aka tura wannan jirgin zuwa kasar Spain domin kula da lafiyarsa, yayin da aka zargi Obiang da sayar da shi ga kamfanin Binter Technic, mai kula da lafiyar jirage a Las Palmas da ke tsibirin Grand Canary a Spain din. Jirgin dai na daukar fasinjoji 74 kuma tun a tsakan-kanin shekara ta 1980, kamfanin ATR na hadin guiwa tsakanin Italiya da Faransa ya kera shi. Da ma dai  Equatorial Guine ta yi kaurin suna a fannin cin hanci da rashawa, inda kungiyar Transparency International ta ayyan...