Posts

Showing posts with the label Tallafin azumi

Abdulmumin Kofa ya raba gagarumin tallafin azumi ga mutum 10,000 a Kiru da Bebeji

Image
Kamar yadda ya saba, Mai Girma Dan Majalisar Wakilai na mazaɓar Kiru/Bebeji, Kano, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa PhD (Jarman Bebeji), ya raba tallafi ga al’ummar yankinsa domin rage musu radadin rayuwa, musamman a watan azumin Ramadan.  A wannan karon, Mai Girma Hon. Kofa ya raba tallafin kudade ga mata da maza har mutum dubu goma. Daga ciki akwai waɗanda suka samu tallafin ₦200,000, da masu ₦100,000, da masu ₦50,000, sai masu ₦20,000 da kuma masu ₦10,000.  Baya ga haka, matasa dubu biyu sun samu damar cin gajiyar shirin tallafin rabon kayan sana’a da zai taimaka musu wajen dogaro da kawunansu Allah ya sada mu da alkhairan da ke cikin wannan watan na Ramadan mai albarka. Amin.