Posts

Showing posts with the label ce-ce-kuce

Za A Kashe N61m Wajen Binne Mutum 103 Da Aka Kashe A Zanga-Zangar #EndSARS A Legas

Image
  Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce bayan Gwamnatin Jihar Legas ta amince ta kashe Naira miliyan 61.2 domin binne mutum 103 da aka kashe yayin zanga-zangar #EndSARS a Jihar shekara uku da suka wuce. A baya dai, gwamnatin Jihar da ma sojoji sun sha karyata rahoton kwamitin jin bahasin da aka kafa kan zanga-zangar, wanda ya ce jami’an tsaro sun bude wuta a kan masu zanga-zangar a Lekki Toll Gate ranar 20 ga watan Oktoban 2020. An dai gudanar da zanga-zangar ce karshen shekara ta 2020, inda wadanda suka yi ta suka nemi a rushe sashen nan na Rundunar ’Yan Sanda mai yaki da ’yan fashi (SARS), saboda kaurin sunan da ya yi  wajen zargin take hakkin dan Adam. Zanga-zangar dai, wacce a lokacin aka shafe tsawon makonni ana yin ta, da farko ta lumana ce, amma daga bisani ta rikide ta koma ta fasawa tare da sace kayayyaki a rumbunan gwamnati da na jama’a, kona ofisoshin ’yan sanda da kuma lalata dukiyoyi masu yawa. To sai dai a wata wasika da idon   Aminiya   ya gani dauke da kwanan wa...