Posts

Showing posts with the label Malam Garba Shehu

Dokar Zabe Ta Inganta Zabukan Najeriya —Fadar Shugaban Kasa

Image
  Fadar Shugaban Kasa ta ce zabukan da aka yi na Shugaban Kasa da ’yan Majalisar Dokokin Tarayya a ranar 25 ga watan Fabarairu, sun inganta ne albarkacin Dokar Zabe ta 2022. Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu, ya ce albarkacin Dokar Zabe, an samu gagarumin ci gaba idan aka kwatanta da zabukan da aka yi a kasar a baya. A sanarwa da kakakin shugaba Buhari ya fitar, fadar ta ce duk da cewa an samu wasu matsaloli nan da can, wannan ba zai sa a ce zaben ya gaza ba. Fadar shugaban ta nuna godiya kan damuwar da manyan jagororin masu sanya ido na kasashen waje musamman tsoffin jakadu; Mark Green da Johnnie Carson suka nuna a kanmatsalolin da aka samu kan kayan aiki a lokacin zabukan.Sanarwar ta ce duk da ’yan matsalolin da aka samu ba za a ce zaben ya gaza ba, illa dai wadanda suka fadi ne suke nuna gazawarsa. Kakakin ya ce zaben na Najeriya ba shi kadai ba ne ake samun ire-iren wadannan matsaloli abu ne da kusan a kowa ce kasa ake iya samu a zabe. Malam Garba ya ci gaba ...