Posts

Showing posts with the label Zababben Gwamnan Kano

Zababben Gwamnan Kano Ya Nada Mai Lura Da Harkokin Karbar Bakinsa

Image
Zababben Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin Abdullahi Ibrahim Rogo a matsayin babban mai lura da harkokin Karbar bakin sa na lokacin mika mulki. Wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin mika mulki na jihar Kano 2023 NNPP Sanata Dr. Abdullahi Baffa Bichi ta nuna cewa nadin zai fara aiki nan take har zuwa ranar 29 ga watan Mayu 2023. Sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Zababben Gwamnan Jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce nadin nasa ya samo asali ne a bisa tarihi da jajircewarsa da kuma biyayyarsa daga 2019 zuwa 2023. Hon. Rogo ya kammala karatun kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja. Ya yi wasu guraben karatu da suka hada da karatun Difuloma daban-daban  Sabon mai jami'in kula da harkokin Karbar bakin da aka nada ya rike mukaman siyasa da dama kamar Sakatare, Kwamitin riko na rusasshiyar jam’iyyar ANPP na karamar hukumar Dawakin Kudu, mai ba shugaban karamar hukumar shawara ta musamman kan harkokin filay...