Search This Blog

Showing posts with label Karatu. Show all posts
Showing posts with label Karatu. Show all posts

Friday, 17 May 2024

Shafin Karbar Rancen Karatu Zai Fara Aiki Ranar Juma’a —Gwamnati

A ranar Juma’a mai zuwa za a bude shafin neman rancen kudin karatu da Gwamnatin Tarayya ta bude domin dalibai zai fara aiki.


Manajan Daraktan Asusun Lamunin Karatu na Najeriya (NELFUND) Mista Akintunde Sawyerr ne ya bayyana 24 ga Mayu, 2024 a matsayin ranar bude shafin neman rancen kudin karatun ga dalibai.

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Alhamis.


Ya ce masu buฦ™atar rancen za su iya shiga shafin ta www.nelf.gov.ng domin neman wani agaji kuma sai su tuntubi hukumar asusun ta info@nelf.gov.ng.


Ya ce: “Ta shafin, dalibai za su iya samun rance kudin makaranta ba tare da damuwa ba.”

Sanarwar da ke dauke da sa hannun mai kula da harkokin yada labarai da hulda da jama’a na asusun, Nasir Ayitogo, ta ce shafin samar da rancen na da saukin sarrafawa kwarai da gaske.


Manajan Daraktan Asusun Lamunin karatun Najeriya ya shawarci wadanda suka cancanci wannan tallafi su gaggauta cikewa domin su mori tsarin da zai taimaka wa gobensu.
(AMINIYA)


Kada Ku Nemi Na Saki 'Yan Daba - Muhuyi Magaji Ya Gargadi 'Yan Siyasa

Clerics Call, Citizens Cheer: Kano Rallies Behind Muhuyi's Anti-Drug Task Force - By Abba Anwar

Politics apart, if there is anything non-political that can open corridor of victory for the Governor of Kano State,...