GAME DA SHARI’AR ZABEN JIHAR KANO: ABINDA YAI SAURA - Saidu Ahmad Dukawa
Bismillahir Rahmanir Raheem Yau, Juma’a 12/1/2024, Allah ya kawo karshen dakon da aka sha wajen sanin wanene halartaccen Gwamna a Jihar Kano. Ina zaton an dade al’umar Kano, da wadanda suka damu da halin da Kano take ciki a fadin Duniya, ba su shiga zulumi (tension) da fargaba (anxiety) kamar a wadannan watannin da aka gudanar da shari’u a mataki daban daban ba. Alhamdu lillah, Allah ya nunawa wadanda suke raye karshen dambarwar. Muna fatan kada Allah ya sake jarrabar Bayinsa da irin wannan halin. Yanzu abu uku ne suka saurar mana. Abu na farko shine kowa ya karbi hukuncin da zuciya daya. Wandanda suka yi nasara kada su dauka iyawarsu ce, wadanda ba su samu yadda suke so ba kada su dauka wani ne ya janyo musu. Wannan ne zai taimaka wajen kaucewa irin wannan jarrabawar anan gaba. Abu na biyu shine gawmanati da dukufa wajen samar da shugabanci nagari, ba tare da tunanin ramuwar gayya ba, ko wariya, ko wani abu mai kama da haka. Ya kamata a sani cewar gwargwadon yadda al’umma