Shugaba Tinubu Ya Nada Farfesa Pakistan A Matsayin Shugaban Hukumar NAHCON
Shugaba Bola Tinubu ya nada Farfesa Abdullahi Saleh Usman a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), inda ya sauke shugaban da ya gabata, Jalal Arabi, bisa zargin cin hanci da rashawa. Farfesa Pakistan fitaccen malami ne da ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Madina da Jami’ar Peshawar da ke Pakistan. A baya ya taba rike mukamin Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Kano, inda ya samu nasarar kula da ayyukan mafi yawan alhazan kasar nan. A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Ajuri Ngalale ya fitar, majalisar dattawa ta tabbatar da nadin. “Shugaban kasa yana sa ran sabon shugaban NAHCON ya yi aikinsa bisa gaskiya, da rikon amana ga kasa,” in ji sanarwar. Wannan ci gaban dai na zuwa ne bayan da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gurfanar da tsohon Shugaban Hukumar, Jalal Arabi, da Sakataren Hukumar, Abdullahi Kontagora bisa zargin karkatar da wasu sassan N90bn da Gwamnatin Tarayya ta fitar don tallafawa...