Yadda CBN Ya Lashe Amansa Kan Karbar Tsoffin N500 Da N1,000
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya jefa ’yan Najeriya cikin rudani bayan ya fitar da sanarwa masu cin karo da juna kan ci gaba a karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 cikin dan kankanin lokaci. CBN ya lashe amansa ne bayan manyan bankunan kasuwanci irinsu UBA da First Bank sun tura wa abokan huldarsu sakonni cewa za su ci gaba da karbar tsoffin takardun N500 da N1,000. Bankunan sun yi haka ne bayan wata sanarwar da kakakin CBN, Osita Nwanisobi, da ke umartar su da karbar kudin matukar ba su wuce N500,000 ba. Sakonsa ga bankunan ya ce, “Hukunar gudanarwar CBN ta umarce ni in sanar da bankunan kasuwanci cewa su fara karbar tsoffin takardun N500 da N1,000 daga hannun kwastomominsu nan take. “Kwastoma zai iya kai har N500,000 bankin kasuwanci, amma abin da ya haura hakan sai dai ya kai ofishin CBN. “Don haka ana bukatar ku bi wannan umarnin,” in ji wasikar farko da babban bankin ya aike wa manajojin reshe da ayyukan bankunan kasuwancin. Bayan fitowar wasikar, ’yan jarida sun tunt...