An Kama Donald Trump Kan Zargin Aikata Laifuka

An kama Tsohon Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump kan zargin aikata laifuka. An kama shi ne ranar Talata yayin da aka gurfanar da shi a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta Manhattan. An tsare ‘yan sandan da suka yi sanadin mutuwar matashi a Filato ’Yan bindiga sun yi garkuwa da matar Dagaci da danta a Kano Ana zargin tsohon shugaban ne da biyan wata mai fina-finan batsa, Stormy Daniels toshiyar baki don kada ta yi bayani game da alakar nema a tsakaninsu lokacin da yake takarar shugaban kasa a zaben 2016. Shi ne tsohon shugaban Amurka na farko da aka taba kamawa a tarihin kasar. To sai dai, a lokuta da dama Trump ya musanta zargin. Sai dai Trump ya ce duk wadanan tuhume-tuhumen da ake masa ba komai ba ne face yi wa takararsa ta neman wa’adi na biyu zagon kasa. AMINIYA