Kungiyar (Independent Hajj Reporters) Ta Sake Yin Kira GA Hukumomin Najeriya da su fara rajistar maniyyata aikin hajjin 2024 Ba Tare Da Bata Lokaci Ba
Kungiyar fararen hula dake daukar rahotannin aikin Haji da Umrah (Independent Hajj Reporters) ta yi kira ga Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) da Hukumar Alhazai ta Jihohi a Najeriya da su gaggauta fara rajistar maniyyatan da ke son zuwa aikin Hajjin 2024. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin a Abuja, mai dauke da sa hannun kodinetan ta na kasa, Ibrahim Mohammed, ta ce kiran ya zama wajibi saboda sauyin da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta yi a kalandar ayyukan Hajji bayan kammala aikin Hajjin 2023. Bisa kalandar, hukumomi a Masarautar suna sa ran dukkan kasashen da ke halartar aikin Hajji za su kammala dukkan shirye-shiryen aikin Hajjin 2024 gami da biza a watan Maris na shekara mai zuwa. Ma’anar hakan ita ce, dukkan kasashen da ke aikin Hajji za su yi rajistar maniyyata, da karbar kudade da kuma kulla yarjejeniya da masu hidima kafin wannan ranar. HaÆ™iÆ™anin shirye-shiryen aikin Hajji na 2024 bai ba da damar jinkiri ba, musamman a