Hukumar NAHCON Ta Duba Karin Tantina Guda Dubu Goma Da Aka Samarwa Alhazan Najeriya
Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON a yammacin yau ta duba karin tantuna dubu goma da kamfanin Mutawwif ya samar wa Alhazan Najeriya domin rage radadin rashin isassun tantunan da mahajjatan Najeriya ke fuskanta tun lokacin da suka isa tudu da dutsen Muna. ran Litinin Shugaban Hukumar, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan wanda ya jagoranci tawagar jami’an gudanarwar sa domin duba wahalhalun da ake fuskanta, ya ce tabbas matakin zai rage wahalhalun da ake fuskanta, kuma ya yi fatan alhazan da abin ya shafa za su ba da hadin kai ganin cewa kwanaki biyu kacal. zauna Muna saura. Wakilan Kamfanin sun yi alkawarin cewa nan da sa’o’i biyu masu zuwa za a samar da isassun motocin da za su kwashe alhazan da suka makale zuwa sabon filin na Turkiyya. Shugaban ya nuna jin dadinsa bisa yadda Kamfanin ya nuna kulawarsa. Ana sa ran za a kwashe maniyyata daga babban birnin tarayya Abuja da na jihar Kogi, ko kuma mahajjata daga ka fannonin yawon bude ido zuwa sabon wurin. Idan dai za a iya tunawa,