Posts

Showing posts with the label El-rufai

El-Rufai Zai Rushe Kamfanoni 9 Mallakar Makarfi

Image
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya soke lasisin mallakar kamfanoni tara na tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmed Muhammed Makarfi. An kuma shirya rushe kamfanoni tara mallakar tsohon gwamnan Jihar. Aminiya  ta fahimci cewa an kai sanarwar janye  hakkin mallaka ga jami’an kamfanonin da abin ya shafa. Sanarwar ta fito ne daga Daraktan kamfanin rake da ke lamba 11 a Murtala Square, Alhaji Ibrahim Makarfi wanda ya mayar da martani da cewa, “lauyoyinmu za su mayar da martani kan kwace hakkin mallakar kamfanonin”. Sai dai da yake mayar da martani kan soke hakkin mallakar a wani sakon da ya aike wa Sanata Makarfi, ya tabbatar da samun wasikun soke kamfanonin har guda tara. Ya ce, “Akwai babban batu. Muna bukatar ganawa da Ustaz Yunus (SAN) domin mu garzaya kotu don dakatar da gwamnatin jiha; kawai sun aiko mana da takardun soke mallaka guda tara”. Daga cikin kadarorin da abin ya shafa sun hada da filaye guda biyar a Mogadishu, filaye uku a kan titin Kwato, da fili day...

Na Fi Karfin Kujerar Minista A Gwamnatin Tinibu - El-Rufa'i

Image
  Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce ba zai karba ba, ko an nada Ministan Babban Tarayya ba a Gwamnatin Bola Tinubu da za a rantsar ranar 29 ga wata Mayu da muke ciki. Gwamnan ya yi wannan furucin ne a yayin da ake shirye-shiryen rabon mukamai a sabuwar gwamnatani, inda ake hasashen za a nada shi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa ko kuma ministan Abuja. Yakin Sudan: Akwai yiwuwar maniyyata su kara biyan wasu kudin  DAGA LARABA: Zama Da Uwar Miji A Gida Daya: Inda Gizo Ke Saka “Ko an ba ni ministan Abuja ba zan karba ba. Na sha fada cewa ba na maimaita aji, kuma na san akwai matasan suka fi dacewa da kujerar,” in ji shi. Da yake jawabi a wurin taron kaddamar da wani littafi a Abuja ranar Talata, ya bayyana cewa, “Ba zan koma gidan jiya ba. Kai! Tun da na bar Abuja ban sake komawa ba sai a 2016 da aka nada abokin karatuna a matsayin minista, ya bukaci gani na. “Yanzu na tsufa da fita yin rusau, gara a samo matasa masu jini a jika.” Ya ci gaba da cewa, “Nan da kwana...

Gwamnoni Sun Roki Buhari A Ci Gaba Da Amfani Da Tsoffin Kudi

Image
  Gwamnonin Jam’iyyar APC sun bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sa baki a ci gaba da amfani da tsofaffi da kuma sabbin takardun kudi. Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne ya bayyana hakan bayan ganawar sirri da suka yi da shugaban kasa a Abuja. Ya ce yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karbi sama da Naira tiriliyan biyu na tsofaffin kudi, amma iya Naira biliyan 300 kacal ya iya bugawa wanda a cewarsa hakan ba zai wadatar da mutane ba. El-Rufai, wanda ya samu rakiyar takwaransa na Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce kamata ya yi CBN ya buga akalla rabin abin da suka tara. Ya ce gwamnonin jam’iyyar sun shaida wa shugaban kasa wawahalar da talakawa ke sha, da asar kayayyaki da ’yan kasuwa ke yi saboda rashin samun masu sayen kayansu. Ya ba da misali da yadda masu sayar da tumatur suka je Legas da kayansu amma suka lalace saboda mutane ba su da kudin saye. El-Rufai ya ce gwamnonin sun roki shugaban kasa da ya sake duba halin da ake ciki. Ya kara da cewar shugaban ...

Babu Kasar Da Ta Taba Sauya Kudi A Lokacin Zabe Sai Najeriya —El-Rufai

Image
Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewar babu matsala a sauya fasalin takardun kudi, amma duk duniya babu kasar da ta taba sauyawa a lokacin zabe sai Najeriya. El-Rufai ya yi zargin akwai gwamnan da shi kadai ya karbi sabbin kudi har na Naira miliyan 500 a kasar nan Ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, inda ya ce an yi tsarin ne don masu kudi, amma da yawansu tsarin ba zai shafe su ba; zai kare ne a kan talaka. “Babu laifi game da sauya kudi, kowace kasa na yi amma babu inda aka taba sauya kudi a lokacin zabe kuma aka bayar da wa’adi kadan, a ina aka taba yin haka a duniya? “’Yan siyasa da manyan ’yan kasuwa da aka yi tsarin dominsu, suna da hanyoyin da za su samu kudin ba tare da sun wahala ba, wasu daga cikinsu su ke juya bankunan, amma wane hali talakawa da kananan ’yan kasuwa za su shiga? “Duka gwamnonin APC sun gana a kan wannan matsalar, mun ga yadda mutane ke shan wahala, mun goyi bayan sauya kudi amma wa’adin da aka ware ...